Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na kokarin samarwa Sudan Kyakkyawar makoma - 2004-11-18


Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya fara taronsa na kwana biyu a Nairobin Kenya don tunkarar tashin hankalin da ake fama da shi a Sudan da fargabar cewa kasa mafi girma a nahiyar Afirka ka iya fadawa cikin halin rashin doka da oda. Shugaban majalisar na wannan watan, jakadan Amurka John Danforth shi ya bude taron ranar Alhamis a inda ya ce wannan ne karo na hudu tun alif da dari tara da hamsin da biyu da aka yi taron kwamitin sulhun a wajen hedikwatar majalisar da ke New York.

‘’Wannan ya nuna irin sha’awar kwamitin kan halin da Sudan ke ciki da kuma damuwarsa kan makomar Sudan abinda ya nuna ba muna damuwa bane yanzu kawai a’a har ma zuwa gaba don tabbatar da samar da karfarfar kasa mai dorarriyar makoma’’, ya ce. Ana sa ran kwamitin zai gabatar da kuduri a ranar Juma’a kan samar da shirin zaman lafiya cikin sauri don kawo karshen shirin yanzu mai tafiyar hawainiya game da yakin Sudan da ‘yan tawaye na kudancin kasar, yakin da ya jawo mutuwar kusan mutum miliyan daya da rabi. Jami’an diflomasiyyar majalisar dinkin duniya suna fatan kawo karshen rikicin arewa da kudancin kasar da kuma samar da zaman lafiya a yankin Darfur wurin da mutane miliyan daya da rabi suka rasa matsuguni a yakin da ake fafatawa tsakanin dakaru larabawa masu daukan makamai wadanda gwamnati ke marawa baya da kuma kungiyoyin bakaken fata guda biyu.

Babban sakataren majalisar dinkin duniya , Kofi Annan ya gayawa taron cewa Sudan da alama ta kasa kare ‘yan kasarta a Darfur saboda haka yanzu wannan aiki mai nauyi ya fada kan kwamitin.’’Halin da ake ciki yanzu a Sudan yana bukatar kulawarku. Hali mara dadi da ake ciki a Darfur ya faru ne saboda shiryayyiyar manufa ta cin zalin farar hula wanda suka hada da kashe-kashe da fyade. Saboda irin wahalar da ake ciki a yanzu rikicin ya zama abin jan hankali matuka.’’

Babban mai sasantawa na Sudan mataimakin shugaban kasa Ali Osman Taha ya ce gwamnati a shirye ta ke da shirin samar da zaman lafiya a duk bangarorin Sudan.’’ Muna so mu tabbatar da kudurinmu na tabbatar da duk wata tattaunawa cikin sauri don samun cikakkiyar zaman lafiya a kudancin Sudan da duk sauran yankunanta’’, ya ce.

Babban shugaban ‘yan tawayen Sudan, John Garang na kungiyar SPLA ya ce ya yi imani za’a iya kammala tattaunawar samar da zaman lafiya a kudu kafin karshen wannan shekarar amma ya bayyana damuwa kan halin da ake ciki a Darfur.’’ Kasarmu tana cikin wani hali. Yanayin da ake ciki a Darfur na kara kazancewa zuwa matakin rashin doka da oda. Mista Garang ya ce hanya mafi sauki ta samar da zaman lafiya mai dorewa ita ce ta samar da gwamnatin hadin kan kasa wadda za ta kunshi kowa da kowa kuma wannan ce in ji shi za ta hana yaduwar rashin doka da oda zuwa sauran bagarorin kasar Sudan

XS
SM
MD
LG