Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan ta ce an kashe ko an kama yawancin manyan shugabannin 'yan ta'adda na kasar - 2004-11-19


Pakistan ta ce bayan kaddamar da kame-kame kusan dukkanin wadanda ake nema saboda zargin kai hare-haren ta'addanci na siyasa cikin shekaru ukun da suka wuce an kama su ko kuma an kashe su. Ministan watsa labarai na Pakistan, Sheikh Rashid Ahmed ya ce wani babban samame a kwana ukun da suka wuce ya sanya an kama duk yawancin wadanda ake nemansu a cikin kasar.Ya ce kamun wannan makon ya hada da na Osama Nazir wanda ya shirya kai hari kan wani coci a watan Maris na shekara ta dubu biyu da biyu wanda ya kashe 'yan Pakistan uku da Amurkawa uku.

Kuma cikin wadanda aka kama din har da Rana Navid al -Hassan wanda ake zargi ya taimaka wajen dasa bam a karamain ofishin jakadancin Amurka da ke Karachi a dai wannan shekarar. A ranar Alhamis 'yan sanda sun harbe wani mutum wanda ake nema dangane da sace da kuma kisan wani dan jarida dan kasar Amurka, Daniel Pearl.

Bayan samame da kame-kame na 'yan sanda da jami'an aikin leken asiri, Mista Ahmed ya ce yanzu an kashe ko an kama dukkanin 'yan ta'adda da ake nema a Pakistan.'Kusan kashi casa'in da takwas na wadanda ake nema an gano su kuma an kama su' in ji Sheikh Rashid Ahmed.' Wadanda suka rage ba su wuce mutum biyu ba amma kusan duk an kama su.' Ya kuma ce yawancin kungiyoyin 'yan ta'addan suna da dangantaka da juna.

Jerin hare-haren sun hada da yunkurin kashe shugaban Pakistan, Pervez Musharraf da firaminista, Shaukat Aziz da kuma wani babban Janar da ke Karachi. Hukumomin Pakistan sun kama mutane da dama da suke zargi da ayyukan ta'addanci hadda wadanda suke zargin 'yan kungiyar al-Qaida ne a 'yan watannin da suka wuce. An kuma kama wasu shugabannin al-Qaida a cikin shekaru ukun da suka wuce. Amma hukumomin ba su samu nasarar kirki ba a wajen shawo kan rikice-rikicen addini tsakanin mabiya Sunni da 'yan Shi'a na kasar.

XS
SM
MD
LG