Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin duniya na taro da shugabannin larabawa kan Iraq - 2004-11-23


Sakataren harkokin wajen Amurka , Colin Powell da shugabannin duniya suna ci gaba da halartar taron shugabannin larabawa a rana ta biyu ranar talata kan yanayin tsaro da ake ciki da kuma zaben kasar Iraqi. Jami’in kungiyar tarayyar turai ta EU, Javier Solana da sakataren harkokin wajen Amurka , Colin Powell da jami’an Iraqi da na makwabtanta suna yin taron tun ranar litinin a wurin shakatawa na Misra, El-Sheikh kuma sun zayyana kuduri wanda za a fitar a karshen taron wanda ya hada da majalisar dinkin duniya da tarayyar turai da kuma kasar Rasha. Kudurin, na goyon bayan yin zaben Iraqi a ranar talatin ga watan Janairu na sabuwar shekara.

Taron bai sanya ranar janyewar sojojin Amurka daga Iraqi ba amma ya jaddada cewa zamansu ba wai ba shi da iyaka ba ne. A wata sabuwa kuma, wasu ‘yan bindiga dadi sun bindige wani malamin ‘yan Sunni har lahira a garin Miqdadiya a arewacin Bagadaza ranar talata kwana daya bayan da aka harbe wani sanannen malamin ‘yan Sunni a birnin Mosul. Dukkaninsu suna cikin kungiyar malaman Sunni ta kasar wadda ke da fada a ji.

XS
SM
MD
LG