Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana zanga-zanga kan sakamakon zaben Ukraine - 2004-11-23


Dubannin masu zanga-zanga ‘yan Ukraine sun taru a rana ta biyu a garin Kiv suna ci gaba da nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaben kasar da ke nuna cewa dan takara mai goyon bayan Moscow, Viktor Yanukovych shine ya lashe zaben a zagaye na biyu. An tura jami’an tsaro zuwa birnin a lokacin da magoya bayan dan hamayya, Viktor Yushchenko suka sha alwashin ci gaba da zama a babban dandalin birnin duk da irin yanayin kankara da ake fama da shi.

Sakamakon hukuma na ranar lahadi, ya nuna cewa Mista Yanukovych na kan gaba to amma hukumar birnin Kiv ta nemi da majalisar kasa da ta yi watsi da wannan sakamakon. Haka kuma jami’an biranen Lviv da Ivano-Frankivsk su ma sun yi watsi da sakamakon zaben. Sakamakon zaben ya nuna a fili an jefa kuri’u ne a bisa bambancin yankuna a inda Mista Yanukovych ya samu kuri’u daga masu magana da Rashanci da ke gabas shi kuma Yushchenko ya samu daga masu magana da yaran ‘yan Ukraine da ke yamma.

A lokacin da ta ke nuna damuwarta ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta nemi hukumomin Ukraine da su binciki kurakuren da aka yi. Ita ma tarayyar turai ta nemi da a samu bin ba’asi cikin gaggawa.

XS
SM
MD
LG