Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar kula da hana yaduwar makaman kare dangi na sa ido kan Iran - 2004-11-23


Kasar Farisa ta ce ta dakatar da duk wani shirinta na kera makaman kare dangi don girmama yarjejeniyarta da kasashen turai. Mai magana da yawun hukumar, Mark Gwozdecky ya ce jami’an hukumar na duba shirin dakatarwar kuma sun ce Farisa na basu hadin kai.’’ Da alama dakatarwar na aiki amma muna sa ido zuwa wasu ‘yan kwanaki mu gani kafin mu tabbatar da cewa duk kayyayakin shirin wanda sun kai goma sha biyu an jingine su.’’, in ji Mista Gwozdecky.

Mista Gwozdecky ya ce masu sa ido na hukumar sun rurrufe wasu kayayyakin da suka shafi wannan aiki kuma sun dauki kididdigar duk kayayyakin ko da za a dauke wani kafin su sake dawowa. Ya kuma kara da cewa hukumar na kokarin gama aikinsu kafin taron hukumar zartarwarsu a ranar Alhamis wanda zai duba ko za a kai fayal din Farisa gaban kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya don a aza mata takunkumi.

Farisa ta ce ita dai shirinta na nikuliya na samar da makamashi ne. Boye shirin tun sama da shekaru ashirin ya sanya jawo zargin cewa tana kokarin kera makamin kare dangi ne. Ita dai hukumar hana bazuwar makaman kare dangi ta duniya ta tabbatar da cewa kafin wannan dakatarwa na Farisa tuni ta kera kusan tan biyu na sinadarin gas na UF-six wanda za a iya amfani da shi wajen tace ma’adinin uranium don yin amfani da shi wajen makamashin wuraren kera makaman kare dangi .Amma Mista Gwozdecky ya ce shi wannan sinadarin UF-six ba abin hada bam ba ne kuma bai kai adadin da za’a kera makaman kare dangi da shi ba .

XS
SM
MD
LG