Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bama-bamai sun fashe a babban birnin Lao - 2004-11-26


An bayar da labarin fashewar bama-bamai biyu a wajen birnin Lao na Vientiane a lokacin da kasar ke shirin daukar bakuncin wani babban taron kasashen yankin. Wadanda abin ya faru a kan idonsu sun ce fashe-fashen sun faru ne ranar Juma’a a kusa da kan iyakar kasar da Thailand.

Babu labarin asarar rayuka kuma babu bayanin abinda ya jawo wannan fashe-fashen. Laos na shirin karbar bakuncin taron kwana biyu na shugabanni daga kungiyar kasashen kudancin Asiya da Sin da Japan da Koriya ta kudu da India da Australia da kuma New Zealand. Amurka ta yi kashedin cewa ‘yan hamayya da gwamnatin kasar Lao na iya kai hare-haren bama-bamai a Vientiane da wasu wurare a lokacin taron na makon gobe.

XS
SM
MD
LG