Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta arewa na son ci gaba da tattanawa kan shirinta na makaman kare-dangi - 2004-11-26


Shugaban babban taron majalisar dinkin duniya ya gayawa shugaban Koriya ta kudu a birnin Seoul cewa Koriya ta arewa tana son a ci gaba da tattaunawa kan maganar lalata shirye-shiryenta kan kera makaman kare-dangi. Amma shugaban , Jean Ping wanda ya dawo daga Pyongyang ya ce har yanzu Koriya ta arewan ta na da sharuddanta. Shugaban babban taron majalisar ya yi taro da shugabannin Koriya ta kudu wanda suka hada da shugaban kasar , Roh Moo-hyun.

Mista Ping, wanda ministan harkokin kasashen wajen Gabon ne ya dawo ne daga Koriya ta arewa a inda ya ce an shaida masa amincewar Pyongyang na ci gaba da tattaunawa da kasashe shida kan batun lalata ayyukanta na kera makaman kare dangi. An ruwaito Mista Ping na bayyana bukatar Koriya ta arewa a matsayi na gaggawa amma ya ce ta gindaya wasu sharudda. Babu cikakken bayani kan amfanun wannan sanarwa ta Mista Ping kan wannan mataki na Koriya ta arewa. Tun a watan Satumba wannan kasa ta ‘yan gurguzu ta ki amincewa da ta halarci zagaye na hudu na taro kan makaman kare-dangi wanda kasar Sin ta dauki bakuncinsa wanda kuma ya samu halarcin Koriya ta kuda da Japan da Rasha da Amurka.

Pyongyang ta bayar da wasu dalilai kamar su rashin yanayi mai kyau daga bangaren Amurka da kuma dagewarta kan ra’ayinta da bukatar taimako da kuma batun cewa Koriya ta kudu ta yi gwajin abubuwan da suka shafi makaman kare-dangi shekaru ashirin da suka wuce. Har yanzu Koriya ta kudu ta na da kwarin gwiwa, in ji Cho Tae-yong, wanda shine babban darektan hukumar kula da shirin Koriya ta arewa na kera makaman kare-dangi na ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta kudu. Ya kuma ce ‘’ ni ban dauka jawabin Mista Ping ba shi da amfani ba, za mu dauka cewa mai amfani ne. Amma kuma ina so in jaddada cewa ya kamata mu sa wani lokaci don fara tattaunawar cikin gaggawa.' Ma’aikatar harkokin kasashen wajen Amurka ta ce a shirye ta ke da ta koma kan tattaunawar ba tare da aza wasu sharudda ba kuma ta na fatan ita ma Koriya ta arewa za ta bi sahu.

A ranar Al-hamis, mai magana da yawun ma’aikatar harkoikn wajen Sin , Madam Zhangh Qiue ta ce Beijing ba ta da wani tsayayyen lokaci na fara tattaunawar. Ta kuma ce batun ya na da sarkakiya kan abubuwan da za a ba mahimmanci a taron kasashen shida wanda har yanzu ana tattaunawa akai. Akwai karuwar fargaba a yankin ruwan Koriya tun sama da shekaru biyu. Amurka ta ce Pyongyang ta yadda cewa ta na da shiri a boye na inganta ma’adinin Uranium ba bisa ka’ida ba a kokarinta na kera makaman kare-dangi. Hukumar leken asirin Amurka ta CIA a rahotonta ga majalisar dokokin Amurka a wannan makon ta ce akwai alamun Koriya ta arewa na kokarin yin gwajin makami mai linzami mai dauke da makaman kare-dangi wanda zai iya isa tekun Pacific.

XS
SM
MD
LG