Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan hamayyar Ukraine na kara sa matsi - 2004-11-26


‘Yan hamayyar siyasa na Ukraine na kara sa matsi a fafutukar ganin an bayyana dan takararsu, Viktor Yushchenko a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar. Suna amfani da hanyoyi da dama wajen ganin sun cimma burinsu wanda suka hada da zanga-zanga a kan titi da kuma kokarin kiran yajin aikin gama-gari da kuma zuwa kotu.

An kiyasta cewa mutane kusan miliyan daya ne ke kan titina don yin zanga-zanga a kokarinsu na ganin an bayyana Mista Yushchenko wanda su ke kira shugaban jama’a a matsayin shugaban da ya lashe zaben. Magoya bayan ‘dan hamayyar sun ce an tafka magudi a zaben wanda ya sanya su shigar da kara a babbar kotun kolin kasar. Da dama daga cikin masu zanga-zangar sun ce ba za su koma aiki ba har sai an bayyana Yushchenko a matsayin shugaban kasa. Wani mai aiki a wani banki ya shaidawa wakilin Muryar Amurka cewa mafi yawancin abokan aikinsa sun shiga zanga-zangar.

A wata sabuwa kuma, daruruwan ma’aikatan hakar kwal daga gabashin Ukraine wanda su ke goyon bayan gwamnati suna cudanya da ‘yan hamayya masu zanga-zangar abinda ya jawo misayar yawu a tsakaninsu. Mahakan wadanda aka ce yawansu ya kai daruruwa sun yi layi sun kuma doshi babban ofisin hukumar zaben kasar a lokacin da su kuma magoya bayan Yushchenko su kuma suka tsai-tsaya a kowane,gefen hanyar suna yi musu ihu.

XS
SM
MD
LG