Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An nemi 'yan hamayyar Ukraine da su ci gaba da zanga-zanga - 2004-11-29


Shugaban ‘yan hamayyar Ukraine mai samun goyon bayan kasashen yamma,Viktor Yushhenko ya yi kira ga magoya bayansa da su ci gaba da zanga-zanga a kan titina wanda suka yi mako guda suna yi kan kin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar. Shi kuwa dan takarar da Rasha ke marawa baya wanda kuma aka ce shine ya lashe zaben suna taro da shugabannin yankunan gabas da na kudu wadanda ke barazanar neman ‘yancin gashin kan yankunansu.

Mista Yushchenko ya je dandalin ‘yanci na Kiev tare da uwargidansa da kuma ‘ya’yansa mata uku don godewa dubannin magoya bayansa saboda irin sadaukar da kansu a kan titina. Ya tunatar da masu zanga-zangar cewa wani lokaci dimukuradiya na daukar lokaci ya kuma bayar da misali da zanga-zangar da ta kawar da gwamnatin Georgia ta tsohuwar tarayyar Soviet wanda ya dauki mako uku. Magoya bayan Mista Yushchenko sun samu karin kwarin gwiwa ranar asabar a lokacin da majalisar Ukraine ta yanke kudurin watsi da sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, sai da kudurin ba shi da tasiri. Haka kuma ‘yan majalisar sun kada kuri’ar yin Allah wadai da hukumar zaben kasar wadda ta bayyana nasarar firaminista ,Viktor Yanukovych mai samun goyon bayan Rasha a matsayin wanda ya lashe zaben.

Mista Yushchenko ya nemi magoya bayansa da su ci gaba da zama a kan titinan birnin kasar da sauran birane har sai an samu nasara. Ya kuma ce masu zanga –zangar sun nuna bajinta ganin irin yawansu amma ya ce babbar bajintarsu ita ce ta gudanar da zanga-zangar cikin lumana.

Shi kuwa Mista Yanukovych yana taro da magoya bayansa a yankin gabashin Ukraine wadanda suka yi barazanar neman ‘yancin gashin kansu muddin Mista Yushchenko ya karbi ragamar mulkin kasar, barazanar da Yushchenko ya kira barazan ga Ukraine a lokacin da ya ke jawabi ga magoya bayansa a Kiev. Mista Yushchenko ya ce tsarin mulkin Ukraine ya bayyana a fili cewa duk wasu masu yin irin wannan barazana a hukuntasu domin suna yin barazana ne da tsaron kasa. Ya kuma nemi da Ukraine da ta samu kyakkyawar dangantaka da kasashen turai da kuma Rasha a inda ya ce ba zai yiwu ba a ce daya daga cikinsu ce za ta yanke abinda ke faruwa a Ukraine.

A wasu jawabai daban –daban , shugaban Ukraine mai barin gado, Leonid Kuchma ya yi kashedin cewa barazanar neman ‘yancin gashin kai ya saba tsarin mulkin Ukraine ya kuma ce tattaunawa ce hanyar samun mafita daga cikin wannan rikicin.Hankali kan wannan rikicin zabe ya koma kan babbar kotun kolin kasar wadda za ta fara sauraren karar ‘yan hamayya a ranar litinin, wadanda su ke zargin an tafka magudi a zaben

XS
SM
MD
LG