Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta nemi Kofi Annan da ya fitar da bayani kan kudin samawa Iraqi abinci - 2004-12-01


Wakilin Amurka a majalisar dinkin duniya ya nemi babban sakataren majalisar, Mista Kofi Annan da ya fitar da dukkanin bayanai kan abin kunyan karkata kudin man Iraqi don sayo mata abinci cikin gaggawa. A karshen makon jiya ne majalisar ta samu kanta cikin zargin cewa daya daga cikin’yan kwangilar ya ba da wasu kudade akai-akai ga dan Mista Annan.

Wakilin Amurkan, Ambasada John Daforth sun yi tattaunawar sirri da sakataren ranar litinin kan maganar binciken wannan batu na karakata kudin man Iraqi na sayo abinci. Wannan ganawa ta zo a lokacin da ake zargin dan Mista Annan dan shekara ashirin da bakwai, Kojo Annan da karbar kudi kowane wata daga wani kamfani na Swiss mai suna Cotecna har zuwa watan Fabarairu na wannan shekarar. Yawanci a wancan lokacin kamfanin Cotecna ya samu kwangila mai tsoka ta duba shirin sayar da man Iraqi don samar mata da abinci. A baya dai, jami’an majalisar dinkin duniya sun ce dan Mista Annan din yana aiki ne da wannan kamfani a lokacin da ya samu kwangilar a alif da dari tara da casa’in da takwas.

Ambasada Danforth ya ce zargin ha’incin a wannan shirin samar da abinci abu ne babba ya kuma nemi da babban sakataren da ya fitar da bayani kan maganar cikin gaggawa.’’ Ya kamata a fitar da dukkanin bayanai filla-filla don mutane su gani da kuma kasashen duniya amma a zahiri Amurka ta gamsu babu wata rufa-rufa domin komai yana nan an bincika shi kuma bani da wani zargi’’

Sakataren majalisar kuwa, Mista Kofi Annan ya gayawa ‘yan jaridu a ranar litinin cewa ya ji takaici da jin cewa dansa ya karbi dala dubu talatin a shekara daga kamfanin Cotecna wanda ya jawo zarge-zarge amma ya ce ba shi da masaniya a kai.’’Dan kasuwa ne mai rike da kansa kuma ya girma ba na shiga harkokinsa shi kuma ba ya shiga na wa. Kuma kamar yadda na fada ba na shiga harkar bayar da kwangila Koma wadanne iri ne', in ji Annan

A farkon wannan shekarar ne Annan ya nada tsohon gwamnan babban bankin Amurka, Paul Volcker da ya binciki zargin cin hanci da rashawa a harkar samarwa da Iraqi abinci. Mista Volcker ya ki yin bayani kan abin da binciken ya gano yana cewa sai ya gama binciken gaba daya. Amma Ambasada Danforth ya nemi Kofi Annan da ya ba da hadin kai ga binciken da majalisar dokokin Amurka ke yi kan lamarin. Shi dai babban sakataren majalisar dinkin duniyar , Kofi Annan ya ki bayar da amsa ga wani dan jarida kan ko zai sauka daga mukaminsa saboda wannan zargi a inda ya ce yanayin da ake ciki yanzu ya hana shi samun damar cimma burinsa na kawo manya-manyan sauye-sauye a harkar gudanar da majalisar. Wani kwamiti na mashahuran mutane da ya kafa a bara don kawo manya-manyan sauye-sauye a majalisar wanda ya hada da kara fadada kwamitin sulhu zai mika rahotansa a wannan makon.

XS
SM
MD
LG