Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsananciyar iska ta kashe daruruwan mutane a arewacin Philippines - 2004-12-02


Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon matsananciyar iska a arewa-maso gabashin Philipinnes bayan da aka kwashe dubannin mutane daga gidajensu. Yankin da bai dadewa da farfadowa daga bala’in muguwar iska ba har sau uku ya sake haduwa da wannan bala’in ranar Alhamis. Ita wannan iska da ake kira Typhoon Nanmadol ta hudu a karfi ta afkawa yankuna shida a cikin mako biyu.

Sakataren cikin gida, Angelo Reyes ya nemi mutane da su zauna a matsugunan da gwamnati ta ware su kuma tanadi abinci da abubuwan da suka dace. Iyalai suna ta kokari cikin iska mai karfi da ruwan sama don komawa wurare masu tudu a yankin Gabaldon a Nueva Ecija na arewacin kasar. Dubannin iyalai tuni suna taru a wuraren da aka samar don tara mutane kuma tuni an umarci sojoji da su fitar da sauran mutane daga yankin.

Darurwan mutane sun mutu sakamakon ballewar tafkuna da ambaliya sakamakon karfin ruwa sama ana kuma sa ran karuwar mace-mace a yankin. Irin matsanancin yanayin da ake fama da shi ya sanya har yanzu an kasa gano sauran mutanen da suka bace.Tes Usapin, wadda ta yi magana a madadin kungiyar agaji ta Red Cross ta ce yanayin ba a taba ganin irinsa ba kuma kungiyarta na tsakiyar aikin ba da agaji a yankin amma ta ce kayan agaji na yin karanci. Ta ce, ‘’ yanzu muka fara aikin amma mun san kayan agajinmu ya kusa karewa shine ya sa muke bukatar taimako cikin gaggawa.’’ Ita dai kasar Philppines ta saba fuskantar irin wannan iska mai karfi a duk shekara amma kuma a samu hudu a cikin shekara guda abu ne da ba a saba gani ba. Shugaba Gloria Arroyo ta ba da umarnin hana sarar manyan itatuwa ba bisa ka’ida ba don yana daya daga cikin abinda yake kawo ambaliyar ruwa mai hatsari. Idan babu bishiyoyi a kan tuddai babu abinda zai rage gudun ruwa da laka zuwa cikin kauyuka.

>

XS
SM
MD
LG