Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe mutum ashirin a hare-haren 'yan tawayen Iraqi - 2004-12-03


Akalla mutane ashirin aka kashe a hare-hare guda biyu na 'yan tawayen Iraqi. Hukumomin Iraqi sun ce 'yan tawayen sun farma ofishin 'yan sanda a yammacin yankin Amil da safiyar Juma'a a inda suka kashe 'yan sanda shida. Daga baya kuma an sake kashe wasu mutane goma sha hudu aka kuma raunata goma sha tara a harin bam da aka kai cikin wata mota wadda ke wajen wani Masallaci a arewacin yankin al-Adamiya. Wadannan hare-hare, su ne na baya-baya daga 'yan tawayen da ke yakar sojojin kawance da Amurka ke jagora da kuma jami'an tsaron gwamnatin rikon kwaryar Iraqi.

Shugaba Bush ya ce ya kamata Iraqi ta tabbatar da aiwatar da zaben da aka tsara za a yi a kasar a cikin watan Janairu duk da kiran da wasu 'yan siyasar Iraqi suka yi na a daga zaben har sai yanayin tsaro ya inganta. A ranar Alhamis ne sakataren tsaron Amurka , Donald Rumsfeld ya amince cewa Amurka ta kasa gano karfin 'yan tawayen Iraqi bayan faduwar gwamnatin Saddam Hussein.

XS
SM
MD
LG