Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kai hari kan karamin ofishin jakadancin Amurka a Jeddah - 2004-12-06


An kai harin bindigogi kan karamin ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Jeddah mai tashar jiragen ruwa na Saudi Arabia. Jami'an Amurka da ke kasar sun ce an kai hari ne kan ofishin. Wadanda abin ya faru a kan idonsu sun ce wuta na ci a harabar ginin bayan da hayaki ya turnuke sama a kusa da ofishin. Wata majiya daga kamfanin dillancin labaran Associated Press ta ce wata karamar mota ce dauke da abubuwan fashewa ta yi bindiga a kusa da ofishin.

Shi kuwa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa ya yi wasu masu kai hari ne suka shiga harabar ofishin suka jefa gurneti. Motocin daukar marasa lafiya sun isa wurin amma babu cikakken bayani kan mutanen da suka mutu. Wani mai magana da yawun Amurka a Riyadh ya ce babu rahotan mutuwar wani Ba-amurke. Ofishin jakadancin Amurka a Riyadh da Dhahran sun rufe kofofin shiga harabarsu daga samun labarin wannan hari na Jeddah.

XS
SM
MD
LG