Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana zaben shugaban kasa a Ghana - 2004-12-07


An fara zaben shugaban kasa a Ghana, na hudu tun da aka fara tsarin jami'yyu da dama a alif da dari tara da casa’in da biyu. An kafa layukan kada kuri'u a tasoshin zabe dubu ashirin da daya tun da sassafe a duk fadin kasar. Ana dai yin zaben shugaban kasa da na'yan majalisar kasa dari biyu da talatin.

Kodayake shugaban kasar wanda ke kan gado, John Kufuor na jam'iyyar New Patriotic ake sa ran zai sake samun wa'adi na biyu na shekaru hudu a zangon karshe akwai goyon baya mai karfi ga abokin hamayyarsa, John Evans Atta Mills na National Democratic Congress. Wani tsohon soja a wata tashar zabe, Peter Kotey ya ce ya tashi awa uku kafin zaben don ya samu damar jefa kuri’arsa ga jam’iyyar hamayya .’’ Muna bukatar kawo sauyi. Kafin shekara ta dubu biyu mun samu sauyi yanzu kuma abubuwa sun tsananta.Tattalin arzikin kasa ya lalace, babu kudi a hannun jama’a,’’ in ji shi.

A lokacin wancan zaben, shugaba Kufuor ya samu hamayya daga Atta Mills, tsohon mataimakin shugaban kasa karkashin Rawlings ya kuma samu nasarar ne a zagaye na biyu. Tattalin arziki shine babban batu a kasa ta biyu a noman koko a duniya. Duk da cewa noman wannan shekarar ya fi na ‘yan shekarun baya ‘yan hamayya suna cewa wannan bai amfani yawancin mutanen kasar ba. Masu jefa kuri’a sun tsaya a layuka a inda magoya baya ke sanye da kananan riguna masu launin tutocin jam’iyyunsu. Kwana daya kafin zaben ‘yan hamayya sun yi zargin cewa an yi shirin yin magudi bayan da suka yi zargin cewa an yi san rai a rajistar masu zaben. Amma wani malamin zabe a wata tashar zabe, Ernest Dameh ya ce sun koyi abubuwa daga zabunan baya guda uku kuma suna daukar matakan tabbatar da gaskiya a zaben. 'A tebirin farko ake rajista, a yi alama kan sunan mutum kuma sai an duba katin shaidar mutum sannan sai a je kan tebiri na gaba inda za a shafawa mai zabe inki don gudun sake yin zaben, ' ya ce.

Masu sa ido kan harkokin zabe daga tarayyar Afirka da tarayyar Turai da kasar Amurka da kuma gamayyar tattalin arziki ta Afirka ta yamma suna zagawa tasoshin zabe don hana magudi. Akwai dai mutane milyan goma wadanda aka yi wa rajista a wannan zaben maimakon miliyan shida da suka yi zaben a shekara ta dubu biyu. Rabin mutanen Ghana an yi musu rajistar yin zaben.

XS
SM
MD
LG