Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan ya yi watsi da kiran da ya yi murabus - 2004-12-08


Babban sakataren majalisar dinkin duniya, Kofi Annan ya ce zai ci gaba da aikinsa duk da kiran da ya yi murabus daga kan mukaminsa daga ‘yan majalisar dokokin Amurka da kuma wasu kafofin watsa labarai.

Shugabannin kasashen duniya da dama suna goyon bayansa a lokacin da ake zargin cin hanci da rashawa a harkar sayar da man Iraqi don sama mata abinci. Kwana daya bayan da wasu ‘yan Republicans suka nemi da Kofi Annan ya yi murabus, babban sakataren ya gayawa wasu ‘yan jarida cewa zai ci gaba da gudanar da aikinsa.’’ Ina da ayyuka da yawa kuma zan ci gaba da wannan ayyuka. Muna da buri babba na kawo sauye-sauye a wannan majalisar. Saboda haka za mu ci gaba da aiki’’, in ji Annan.

Ana yin korafi ne kan Annan saboda abin kunyan karbar cin hanci da ya shafi dansa , Kojo Annan daga wani dan kwangila a harkar sayar da man Iraqi don sama mata abinci. Wannan batu ya jawo kiran da ya yi murabus daga wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka da wasu kafofin watsa labarai. Shugaban kwamitin majalisar dattijan Amurka da ke bincikar batun ya yi zargin cewa Annan na hana ruwa gudu a binciken majalisar.

Amma a wajen sauran kasashe, Mista Annan yana samun goyon bayansu. Shugabannin kasashen Faransa da Spain sun buga masa waya suna yabawa jagorancinsa. Tarayyar Afirka ta fitar da sanarwa a ranar talata tana nuna goyon bayanta ga Annan a madadin dukkanin ‘yan kungiyar. Kafin wannan, firaministan Birtaniya ,Tony Blair ya yabawa Annan yana cewa kushewar da ake masa ba ta dace ba. Rasha da China su ma sun tabbatar da goyon bayansu ga shugabancin Annan. A wata hira da ‘yan jaridu , sakataren harkokin wajen Amurka, Mista Colin Powell ya kira Mista Annan a matsayin babban sakatare nagari. Amma gwamnatin Bush ta ki shiga yabon da ake wa Annan. A ranar talata, jakadan Amurka a majalisar dinkin duniya, Ambasada John Danforth ya ce akwai bambanci tsakanin auna aikin Annan a matsayin babbabn sakatare da kuma maganar binciken samawa Iraqi abinci. Babban sakataren ya kafa kwamitin bincike a farkon wannan shekarar karkashin tsohon gwamnan babban bankin Amurka, Paul Volcker domin gano ainihin gaskiyar abinda ya faru.

Mista Volcker ya ce yana sa ran mika rahotansa a watan Janairu. Rahotan zai yi bayani kan zargin cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatan majalisar dinkin duniya. Rahoto na biyu za a mika shi daga baya, zai kuma yi bayani kan ko tsohon shugaban Iraqi ya yi amfani da shirin jin kai na samar da abinci don sayan makamai da kuma samun goyon baya. Shirin majalisar dinkin duniyan ya bawa Iraqi damar sayar da manta don sayan abinci da wasu abubuwan yau-da –kullum. Amma an dakatar da shirin a shekarar da ta wuce.

XS
SM
MD
LG