Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Amurka ta tura sabuwar dokar tsaro zuwa - 2004-12-09


Majalisar dattijan Amurka ta ba da amincewar karshe ga dokar manya–manyan sauye-sauye kan aikin tattara bayanan sirri a ranar laraba , kwana daya bayan da majalisar dokoki ta amince da dokar. An samu kuri’ u tamanin da tara masu goyon baya, guda biyu kuma wanda ba sa goyon baya. Yanzu dokar za a kai ta gaban shugaba Bush don rattaba hannu.

Dokar ta samar da manya–manyan sauye-sauye a harkar aikin asiri a Amurka tun sama da shekaru hamsin da suka wuce. Dokar na kunshe da yawancin shawarwarin hukumar da ta binciki harin ta’addancin da aka kai Amurka a shekara ta dubu biyu da daya. Ta kuma nemi da a nada babban darektan aikin asiri da kuma samar da cibiyar yaki da ta’addanci don tattara da musayar bayanan sirri. Senata Susan Collins ‘yar jam’iyyar Republican daga Maine ita ce ta gabatar da batun dokar a inda ta ce,’’ Ba na ce wannan dokar za ta hana kawo harin ta’addanci kan Amurka ba ne, amma za ta taimakawa hukumomin leken asiri samun damar yin aikinsu kuma za ta sanya mu kara ganowa da kuma karewa ko kuma ma mayar da martani kan hari ga kasarmu.’’

Dokar ta dauki watanni ana sauraronta da kuma tattaunawa mai zafi. ‘Yan kwanaki da suka wuce dokar ta so ta hadu da cikas a inda ‘yan majalisar dokoki suka nuna rashin amincewa da ita. Amma bayan matsi daga shugaba Bush ‘yan majalisar suka daidata musamman kan batun cewa kwamandojin yaki za su samu damar samun bayanan sirri. Duk da haka, ‘yan majalisar suna da damuwa kan sabuwar dokar. Senata Ted Stevens dan Repulican daga Alaska wanda ya goyi bayan dokar ya ce, babban darektan aikin asirin zai samu wani karfi mai yawa. ‘’Shi wannan darektan ba zababbe ba ne kuma ba shi da dangantaka ta kai tsaye da Amurkawa. Darektan zai zama yana bayani ne kawai ga shugaban kasa abinda zai karawa shugaban aiki na duba shi.’’ Senata Carl Levin na Democrat daga Michigan wanda bai goyi bayan dokar ba, ya kushe dokar saboda cire sashen da ya nemi babban darektan da ya zama yana da cin gashin kai daga fadar gwamnati ta White House.

Senata Robert Byrd na Democrat daga West Virginia wanda shi ma bai goyi bayan dokar ba ya ce, majalisun sun yi gaggawa wajen amincewa da dokar ba tare da isasshiyar mahawara ba.’’ Ba mu sani ba ko za ta taimakawa gwamnati ko hukumomin aikin leken asiri su kare abkuwar hare-hare ko kuma za ta jawo wasu matsaloli da ba a zata ba. Mun gaza wajen yin nazari ta yin gaggawa, ‘’ in ji shi

Wasu ‘yan majalisar sun ce dokar ta kasa maganta matsalar tsauraran ka’idojin shige da fice da kuma musamman kasa hana bakin haure marasa izini wanda ya hada da wadanda ka iya zama ‘yan ta’adda samun lasisin tuki da wasu takardun sheda. Dan majalisa James Sensenbrenner na Republican daga Wisconsin ya gabatar da shawara don ta magance wadannan abubuwa a ranar laraba. Duk da cewa ‘yan majalisa da dama sun yadda cewa akwai ‘yan kura-kurai a dokar amma sun amince cewa dokar ta zama dole. Mai magana da yawun fadar White House ya ce shugaba Bush na fatan sanya hannu a kan dokar ya kuma ce za ta tabbatar da tsaron Amurka.

XS
SM
MD
LG