Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila na kokarin kafa gwamnatin kawance - 2004-12-10


Jam 'iyyar firaministan Isra'ila, Ariel Sharon a ranar Alhamis ta jefa kuri'ar amincewa da kafa gwamnatin kawance a kokarin cimma burin janyewar kasar daga zirin Gaza. Mista Sharon ya nemi 'yan jam'iyyarsa da su amince da kawancen da jam'yyar hamayya ta Leba yana cewa wannnan zai taimaka wajen samun goyon baya ga gwamnati a shirinta na janyewa.

A wata sabuwa kuma, jami'an sojan Isra'ila sun ce sun kashe Palasdinawa biyar a wasu hadarurruka daban -daban guda biyu a kan iyakar kasar da Misra a kusa da zirin Gaza a daren jiya. Sojojin sun bude wuta a kan wasu mutane masu tafiya cikin kungiya a wurin da aka hana bi kusa da Rafah a inda suka kashe mutum uku. Jami'an sojan sun ce sojojin sun dauka 'yan fasa kwauri ne ko 'yan ta'addda masu shirin kai hari.

Haka kuma sojojin Isra'ila sun harbe wani dan Palasdinu har lahira suka kuma raunata guda biyu a wurare daban-daban kusa da kan iyakar Gaza. Dayan da aka raunata ya rasu a asibiti daga baya.

XS
SM
MD
LG