Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Karzai ya nemi ‘yan Iraqi da su shiga zaben kasarsu - 2004-12-13


Kasa da mako daya da rantsar da shi a matsayin zababben shugaban Afghanistan na farko, Hamid Karzai ya shawarci mutanen Iraqi masu shirin shiga zabe a watan gobe da su bi sahun kasarsa wajen zabar gwamnati ba tare da tashin hankali ba. A ranar lahadi ne a shirin gidan talabijin na CNN, shugaba Karzai ya bayar da wannan shawarar a inda kuma ya yi tir da hare-haren da ake kai wa a cikin kasar ya kuma yi kira ga ‘yan Iraqi da su daina taimakawa mayaka ‘yan kasashen waje.

‘’ Mutanen Iraqi ba su da wata riba idan suka kyale irin wadannan mutane daga kasashen waje suka bata musu rayuwarsu. Dole ne su shiga zabe, su kuma yi amfani da wannan dama wajen zabar mutanen da za su je majalisa su kuma samu gwamnatin kansu don samun zaman lafiya. Wannan shine abinda ya dace da su, kuma ita ce mafita a garesu.’’ Ya ce. A lokacin hirar, an tambayi Mista Karzai kan wasikar da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta fitar a farkon wannan watan kan zargin keta hakkin da sojojin Amurka ke yi wa ‘yan Afghanistan da ake tsare da su.

Shugaba Karzai ya ce ya yi imani mutanen Afghanistan sun yadda dimukuradiyyar da su ke amfana yanzu sakamakon sadaukarwa ne na rayukan ‘yan Afghanistan da Amurkawa. Amma ya ce sabuwar gwamnatinsa za ta binciki zargin da zarar ta zauna da gindinta. ‘’Mun tattauna da gwamnatin Amurka da dakarun Amurka da jakadan Amurka a nan. Kuma akwai daidaituwa a kai. Muna kokarin inganta yanayin. Muna duba batun kuma za a samu daidaitawa, ‘’ in ji shi. Da aka tambaye shi ko gwamnatinsa ta kusa kama Osama Bin Laden sai ya ce i kuma a’a.

‘’A bangaren nasarorin kasar da kuma kawancen yaki da ta’addanci kwarai mun kusa. A maganar kama shi kuwa to sai dai mu yi fatan sa’a mu kuma ci gaba da nemansa,’’ ya ce.

Shi dai Osama ana zaton yana boye ne a kan iyakar Afghanistan da Pakistan. Mista Karzai ya godewa Pakistan saboda irin kokarinta a wannan batu. A wata sabuwa kuma shugaba Karzai ya ce gwamnatinsa ta damu matuka kan noman tsiran opium wanda majalisar dinkin duniya ta ce shi ke samar da kashi biyu cikin uku na arzikin kasar. Ya ce mutanen kasar suna damuwa kan cewa kasarsu ce ke noma opium wanda ake amfani da shi wajen samar da kayan sa maye. Ya kuma ce a cikin matakan da gwamnatinsa za ta dauka har da lalata gonakin nomanta a inda za a sauya abinda ake nomawa a cikinsu.

XS
SM
MD
LG