Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin kunar bakin wake ya kashe mutum bakwai a Iraqi - 2004-12-13


Akalla mutane shida ne suka halaka wasu sama da goma sha biyu kuma suka raunata sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai cikin mota kan wani wurin duba motoci a tsakiyar Bagadaza ranar litinin. Harin ya abku ne a lokacin bikin cika shekara daya da kama tsohon shugaban Iraqi, Saddam Hussein.

Karar fashewar nakiyar, an ji ta a kusan duk fadin Bagadaza. Ya kuma abku ne da misalin karfe tara na safe a yankin da ake kira Green Zone, yankin da ya kunshi ofishin gwamnatin rikon kwarya da kuma ofisoshin jakadancin kasashen waje. Yankin shine ya fi ko’ina samun tsaro a Bagadaza.

Jami’an gwamnati sun ce wata motar wani dan kunar bakin wake wadda ke jira a layin duba motoci ce ta fasa nakiya abinda ya jawo lalacewar sauran motoci. Hadarin ya abku a lokacin da ‘yan Iraqi ke kokarin zuwa aiki a yankin. Wuraren duba motoci suna daya daga cikin wuraren da ‘yan tawaye ke kai wa hare-hare a yankin a kokarinsu na hana yin zaben da aka shirya yi a watan gobe. Amma wani jami’in gwamnatin rikon kwarya ya ce harin na ranar litinin ba ya rasa nasaba da bikin cika shekara daya da kama Saddam Hussein wanda ya faru ranar sha uku ga watan Disamban bara.

Wannan jami’i ya kuma ce hare-haren sun yi yawa tun bayan wancan lokaci fiye da yadda kowa ya yi zato. Amma ya ce za a shawo kan wannan hare-hare kuma za a yi zaben a watan gobe kamar yadda aka tsara. A ranar Asabar, an kashe sojojin kundunbalar Amurka takwas a lardin Anbar wanda ya hada da biranen Fallujah da Ramadi da kuma yammacin Bagadaza. Hukumomin soja sun ce an kashe sojojinne a hare-hare guda biyu daban-daban a lokacin aikin tabbatar da tsaro. Amma sun ki bayar da bayanin yadda suka mutu saboda tsaron sauran sojojin kundunbalar da ke aiki a yankin. Wannan kisan sojojin kundunbala shine mafi yawa a rana daya tun daga lokacin harin da aka kai cikin wata mota a wajen Fallujah a ranar talatin ga watan Oktoba.

Garin Fallujah dai shine inda Amurka ta kai babban farmaki a watan da ya wuce don kwato shi daga hannun ‘yan tawaye. Wannan kisa ya faru ne kwana daya bayan da jiragen yakin Amurka suka kai hari da makami masu linzami kan Fallujah a lokacin da ‘yan tawayen suke fafatawa da dakarun kawance a birnin.

XS
SM
MD
LG