Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rumsfeld na shan suka kan maganganunsa - 2004-12-13


Wasu ‘yan majalisar Amurka na kushe sakataren tsaro, Donald Rumsfeld bisa kalamansa kan samawa sojojin Amurka da ke Iraqi motocin yaki masu sulke. Bacin rai kan yadda ma’aikatar tsaro, ke aiwatar da ayyukan soja a Iraqi na jawo damuwa tsakanin ‘yan Republicans da ‘yan Democrat musamman yadda ake samun karuwar mutuwar dakarun Amurka sakamkon hare-haren ‘yan tawaye.Su kansu ‘yan majalisar da ada su ke goyon bayan Rumsfeld kan al’amuran Iraqi yanzu sun janye goyon bayan.

A ranar laraba, Rumsfeld ya bayar da wata amsa ga wani soja kan menene ya sa mayakan Amurka suka kasa samun isassun motocin yaki masu sulke abinda ya jawo ake kai musu hare-hare, sai ya ba shi amsa kamar haka: ‘’ Za ka iya zuwa yaki da sojojin da ka ke da su amma ba lallai irin wanda ya kamata ka je da su ba .’’

A hira da tashar talabijin ta CNN, Senata Chuck Hagel na Nebraska dan Republicans kuma na hannun daman shugaba Bush ya nuna rashin jin dadi da amsar Rumsfeld. Ya ce, ‘’ wannan soja da sauran sojoji sun cancanci amsa wadda ta fi wannan. Ina mamakin yadda iyayen sojojinmu za su ji, na tabbatar ba za su ji dadinta ba.’’Senata Hagel ya kuma ce a karkashin Rumsfeld ma’aikatar tsaron Amurka ta ki tura isassun dakaru zuwa Iraqi a inda ya yi watsi da shawarar janar-janar kan cewa za a bukaci dakaru masu yawa bayan kawar da Saddam. Wannan sako an sake jaddada shi ta hannun Senata John Corzine na Democrat daga New Jersey wanda ya ce matsalar Amurka a Iraqi ta wuce ta motocin yaki masu sulke. Mista Corzine ya yi magana ne da gidan talabijin na Fox a ranar lahadi.

Ya kuma ce akwai matsalar tattara bayanan asiri kafin yakin, akwai kuma gazawar kwace makamai daga hannun jama’a, akwai matsalar kula da gidajen yari da dai sauransu. ‘’Amma har yanzu babu wanda aka tuhuma kan wadannan matsalolin,’’ in ji shi. Jami’an Amurka sun ce kashi uku cikn hudu na motocin sojojin samfirin Humvees na da sulke. Wani dan jarida wanda ke tare da dakarun Amurka ya ce shine ya koyawa sojan yadda zai yi tambayar da ta zama abar magana kan Rumsfeld. A amsarsa, Rumsfeld ya ce su kansu motocin yaki masu sulke ana iya kai musu harin bama-baman bakin titi da dai sauransu. Tun sama da shekara daya da ta wuce wasu ‘yan Democrat su ke kiran da Rumsfeld ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Da aka tambayi Senata Hagel ko ya goyi bayan shugaba Bush na ci gaba da rike Rumsfeld a matsayin sakataren tsaronsa a karo na biyu sai ya ce, ‘’wannan mataki ne da ya shafe shi. Matakinsa ne kuma shine zai kare wannan matakin, abinda zan iya cewa kenan.’’

XS
SM
MD
LG