Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sake kai harin kunar bakin wake a Iraqi - 2004-12-14


An sake kai wani harin kunar bakin wake da mota mai dauke da bama-bamai a kofar shiga yankin Green Zone mai cike da tsaro na Bagadaza, wanda shine irinsa na biyu a cikin kwana biyu. Majiyoyin asibiti sun ce akalla mutane goma sha biyu ne suka raunata sakamakon wannan hari na ranar talata. Wasu daga cikin wadanda suka samu raunukan an ce suna cikin matasanancin hali.

Jami’an sojan Amurka sun ce harin ya abku ne a dai-dai wurin duba motocin da aka kai harin jiya wanda akalla ya kashe ‘yan Iraqi tara. Kungiyar ‘yan ta’adda ta Abu Musab al- Zarqawi ta ce ita ce ta kai wadannan hare-hare a dai-dai lokacin da ake bikin cika shekara daya da kama tsohon shugaban Iraqi, Saddam Hussein.

An kuma samu labarin samun fadace-fadace a Fallujah, birnin mabiya Sunni , wurin da Amurka ta zafafa hare-hare kan ‘yan tawaye a watan da ya wuce. Ana samun karuwar fadace-fadace a birnin a ‘yan kwanakin nan.

XS
SM
MD
LG