Jami'an tsaron Afghanistan sun kama wani jigon masu yakar dakarun gwamnati a yankin kudancin kasar na Kandahar. Wanda aka kama din ana zarginsa da jagorantar manya-manyan hare-haren ta'addanci cikin 'yan shekarun da suka wuce. Jami'an gwamnatin Afghanistan sun ce wanda suka kama din shine, Mullah Naqibullah Khan, shugaban 'yan tawaye masu biyayya ga tsohuwar gwamnatin Taleban.
Jami'an suka ce an kama shi tare da daya daga cikn mataimakansa , kuma yana dauke da na'urar sadarwa mai aiki da tauraron dan Adam da kuma wasu takardu wadanda ka iya taimakawa wajen sake kama wasu. Mai magana da yawun hukumomin Kandahar, Khalid Pashtoon ya ce 'yan tawayen da ake zargi Mullah Naqibullah ke jagoranta suna babbar barazan ga tsaron yankin ya kuma ce yanzu yanayin zai inganta da ya ke shugabansu na hannu.
' Wata uku zuwa hudu da suka wuce, sun yi wa wata motar karamar hukuma kwantan bauna a inda suka kashe duk mutanen da ke cikinta. Kuma sun kai hare-hare da dama a yankin, 'in ji shi. Mullah Naqibullah ya taba zama shugaban rundunar tsaron lafiyar shugaban 'yan Taleban, Mullah Mohammed Omar, wanda har yanzu ba a kama shi ba. To amma Mista Pashtoon ya ce da alama mutanen biyu ba su hadu ba tun lokacin da dakarun Afghanistan da na Amurka suka hambarar da gwamnatin 'yan Taleban a shekarar dubu biyu da daya.
Ya ce saboda haka ba lalle ne wannan kamu ya kai ga kama Mullah Omar ba wanda Mista Pashtoon ya ce ba lalle ne yana Afghanistan ba. Amma ya ce wannan kamu na Mullah Naqibullah babbar nasara ce ga sabuwar gwamnatin Afghanistan.' Sabuwar gwamnatin dama na neman wannan dan taliki tun sama da shekara daya kuma ga shi mun kama shi daga karshe saboda haka muna murna a kan wannan,' in ji Mista Pashtoon. Magoya bayan Taleban sukan kai hare-haren sari-ka-noke cikin Afghanistan amma hare-haren sun ragu tun daga tsakiyar bara.