Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Amurka sun ce babu cin zarafin tsararru a Afghanistan - 2004-12-15


Hukumar sojin Amurka a Afghanistan ta ce bayan da ta duba wuraren tsare mutane a Afghanistan ba ta samu shaidar cin zarafin wadanda ake tsare da su ba. Wannan bin ba’asi ya biyo bayan zargin cin zarafin tsararrun daga wata kungiyar kare hakkin bil Adama.

Mai magana da yawun sojin Amurka a Afghanistan, Manjo Mark McCann ya ce duba wuraren tsare mutanen ya nuna babu wani cin zarafi ga tsararru a cikin wata bakwai da suka wuce. ‘’ Bincikenmu ya nuna cewa babu alamar cin zarafi ko alamar cewa kwamandoji na sa a ci zarafin tsararru ko kuma suna kyalewa ana cin zarafin,‘’ ya ce. Kalaman Manjo McCann sun biyo bayan rahotan wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amurka, Human Rights Watch wanda ya yi zargin kuntatawa wadanda ake tsare da su ta hanyoyi daban-daban. Ya kuma ce binciken da wani kwamandan sojan Amurka ya kaddamar a Afghanistan a watan Mayu ya binciki yanayin da ake ciki ne yanzu amma bai duba abinda ya faru a baya ba. ‘’

Ba za mu koma baya ba mu sauya yanayin, abinda za mu iya yi shine tabbatar da yanayi mai kyau a yanzu da kuma a nan gaba kuma ya kasance abinda ya faru a baya bai sake faruwa ba,’’ in ji Manjo McCann. Ya kuma ce wannan rahoto na Human Rights Watch zai sanya sojin Amurka fitar da sakamkon bincikenta ga jama’a nan da wani dan lokaci. Mafi yawancin mutanen da ake tsare da su ana zarginsu ne da taimakawa masu kai hare-haren tawaye kan gwamnati. Wasu firsunonin da aka saki sun yi zargin cewa masu tsaronsu sun ci zarafinsu ta hanyar duka ko yin lalata da su. Ita dai Human Rights Watch ta bayar da misalin mutuwar ‘yan Afghanistan takwas a lokacin da suke tsare. Manjo McCann ya ce ana dai biciken wannan mutuwar mutane takwas amma ya ce na guda daya aka gama a yanzu.

A wata sabuwa kuma, a ranar laraba an tsinci gawar wani injiniya dan kasar Turkiya wanda aka sace a gabashin Afghanistan. Da alama an masa harbi da dama bayan da aka sace shi tare da direbansa da kuma mai masa aikin tafinta wadanda aka sake su ba tare da wani lahani ba. Wannan shine karo na biyu da aka kashe injiniya dan kasar Tirkiya wadanda ke aikin gina hanyoyi a Afghanistan.

XS
SM
MD
LG