Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush ya ce zai tabbatar da farfadowar darajar dala - 2004-12-16


Shugaba Bush ya ce zai yi aiki da majalisa dan rage gibin kasafin kudin Amurka a kokarin rage damuwar Turai kan faduwar darajar dala. Mista Bush ya yi magana ne bayan tattaunawa da firaministan Italiya, Silvio Berlusconi. Shugaba Bush ya ce zai ci gaba da kokarin tabbatar da farfado da darajar dalar Amurka tare da sabuwar majalisar kasar ta hanyar aiki tare dan rage gibin kasafin kudi wanda ya ce zai sanya mutane su rinka sayan dalar.

‘’ Mun yi imani cewa kasuwa ita ya kamata ta nuna dangantakar dalar Amurka da takardar kudin euro, ‘’ in ji shugaban. Shugaba Bush ya gana da firaminista Berlusconi kwana daya bayan da Amurka ta bayar da sanarwar samun gibin kasuwanci na dala biliyan hamsin da biyar da digo biyar a watan Oktoba. Wannan ya jawo faduwar darajar dalar Amurka. Wannan ya taimakawa masu masana’antun Amurka saboda kayayyakin Amurka suna da sauki ga masu saya daga kasashen waje. Akwai damuwa a Turai kan matsayin dala domin faduwarta kan fam din ingila da kuma na euro.

Shugaba Bush ya ce matakin da Amurka ta dauka na sake kara yawan kudin da ake caja kan kudin ajiya alama ce ga kasuwannin duniya cewa shugaban hukumar rarar ajiya, Alan Greenspan yana sane da irin darajar kudaden euro da dala. Shugaba Bush ya ce hanya mafi sauki ta kara darajar dalar Amurka ita ce ta magance tsohuwar matsalar karbar bashi wanda ke faruwa sakamakon gibin kasafin kudi. Shugaban ya damu matuka musammanma kan kididdigar abinda za a kashe wajen shirin ritayar ma’aikata. Mista Bush na kokarin shigar da ‘yan kasuwa cikin shirin yadda matasan ma’aikata za su iya zuba kudadensu a cikin harkar kudaden ritayarsu a cibiyoyin kudade. ‘’ Na yi kamfen a kan wannan. Ina fatan yin aiki da majalisa don magance wannan tsohuwar matsala dan cibiyoyin kudi su samu gamsuwa cewa wannan gwamnatin za ta magance matsalar gibin kasafin kudi, ‘’ ya ce. ‘Yan majalisa daga jam’iyyar Democrat ba sa goyon bayan wannan shiri suna cewa zai jawo rage kudaden sallamar Amurkawa tsofaffi ya kuma jawo yin ritayar matasa wadanda za su iya yin asarar kudaden da za su zuba a wasu cibiyoyin kudin.

XS
SM
MD
LG