Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharon na da yakinin samun zaman lafiya duk da - 2004-12-17


Firaministan Isra’ila, Ariel Sharon ya ce yana da yakinin cewa za a samu zaman lafiya a shekara mai zuwa muddin Palasdinawa suka daina kai hare-hare kan Isra’ila. A lokacin da ya ke jawabi a wani taron masana a daren Alhamis a garin gabar ruwan kasar na Herzliya ya ce akwai kyakkyawan fata nan gaba ga Isra’ila da Palasdinawa.

A karon farko kuma ya ce yana son ya tsara shirinsa na janyewa daga yankunan Palasdinawa tare da hadin kan sabuwar gwamnatin Palasdinawan. A baya, firaministan ya yi niyyar aiwatar da tashin dukkanin matsagunan yahudawa na yankin zirin Gaza da kuma guda hudu a yammacin kogin Jordan ba tare da sa Palasdinawa a cikin shirin ba. Ya gayawa taron cewa , ‘’ kasancewar wannan dama a yanzu da kuma alamar samun sabuwar gwamnatin Palasdinawa, Isra’ila a shirye ta ke ta yi tsare-tsaren janyewarta daga yankunansu da sabuwar gwamnati mai zuwa, gwamnatin da za ta karbi wuraren ta kuma kula da su bayan mun bar su.’’

Ministan gwamnatin Palasdinawa, Saeb Erekat wanda shine mai lura da tattaunawa da Isra’ila ya ce wannan jawabi na Sharon babu wani abu sabo a cikinsa. Wani kuma mai magana da yawun kungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta Hamas ya kira jawabin a matsayin ayyana yaki kan Palasdinawa. A wata sabuwa kuma, dakarun Isra’ila sun kai hari a kudancin zirin Gaza a ranar Juma’a kuma sun kashe Palsdinawa biyu suka kuma raunata bakwai wasu kuma da dama suka rasa matsagunai sakamakon rushe musu gidaje.

Harin ya zo ne awanni da dama bayan da jirgin saman yakin Isra’ila ya harba makami mai linzami kan wani shagon ayyuka wurin da sojin Isra’ila suka ce Palasdinawa masu yakin sa kai na amfani da shi wajen ajiye makamai a inda suka lalata shi kodayake babu wanda aka kashe. Palasdinawan da suke wurin lokacin da abin ya faru sun ce wurin, shagon kafintoci ne a yankin ‘yan gudun hijira na Rafah a kan iyakar Gaza da Misra.

XS
SM
MD
LG