Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila ta amince ta sako Palasdinawa dari da saba'in - 2004-12-20


Isra'ila ta amince ta sako Palasdinawa dari da saba'in daga gidan kaso. Sakin wadannan Palasdinawa na daya daga cikin alkawuran da firaministan Isra'ila, Ariel Sharon ya yi wa shugaban kasar Misra, Hosni Mabarak don a sako wani dan kasar Isra'ila wanda aka daure a Misra saboda laifin leken asiri a wannan watan. Ana sa ran za a sako wadannan Palasdinawa a mako mai zuwa.

Har yanzu dai ba a san ko wadanne Palsdinawa za a sako ba, sai dai Isra'ila ta ce ba za ta sako masu hannu a kashe-kashe ba. Jami'an Palasdinawa sun dade suna bukatar da a sako dubannin Palasdinawa da Isra'ila ke tsare da su, sun kuma ce sakin baya na fursunonin bai wadatar ba.

XS
SM
MD
LG