Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush ya ce yana da yakinin samuwar dimukuradiyya a Iraq - 2004-12-21


Shugaba Bush ya ce dole ne a ci gaba da shirin samar da dimukuradiyya a Iraqi duk da irin tashin hankula da ake fama da su da kuma matsalar horar da jami’an tsaron kasar. Kasar Iraqi na daya daga cikin batutuwan da shugaba Bush ya yi magana a kai a lokacin hira da ‘yan jaridu na karshen shekara. Shugaba Bush ya ce dama ba wai ba ya tsammanin samun rikici ba ne a harkar zaben ya kuma ce babu wanda zai iya cewa ga irin iyakacin wahalhalun da za a iya fuskanta wajen samar da dimukuradiyya.

‘’Amma duk da haka na yi imani da sakamakon cewa ‘yan ta’adda ba za su samu nasara ba , kuma za a yi zaben, za a tabbatar da dimukuradiyya a Iraqi wanda zai dace da dabi’u da al’adun mutanen kasar’’, ya ce. Ya kuma lura cewa akwai damuwa kan horar da jami’an tsaron Iraqi da kuma irin illar da hare-haren ‘yan tawayen a wurin mutanen Iraqi da kuma masu lura da abinda ke faruwa a Amurka.

Mista Bush ya ce akwai lokutan da dakarun Iraqi suka gudu daga fagen fama wanda abu ne da bai dace ba amma akwai a wuraren da suka yi kokari wajen fada da ‘yan tawayen masu kai hari a kan ‘yan Iraqin da ba su ji ba su gani ba. ‘’ Harin bama-baman motoci wadanda sukan yi lahani ga yara ko wadanda suka lalata wuraren ibada abu ne na farfaganda. Amma dole ne mu cimma burinmu wanda shine mu taimakawa ‘yan Iraqi su kare kansu kuma su samu tsarin siyasar da zai kai su gaba. Babban burinmu ne mu ga mun samu nasara,’’ ya ce. A lokacin tattunawa da ‘yan jaridun , shugaban ya bayyana fatan samun zaman lafiya a gabas-ta-tsakiya. Ya ce zaben Palasdinawa na watan Janairu mataki ne na farko. Ya kuma yi watsi da masu kushe manufarsa ta samun kasashe biyu. ‘’A yanzu ne ya kamata a ci gaba da kokarin samar da zaman lafiya. Amma babu yadda za mu ce Palsdinawa ba za su mulki kansu ba ko kuma ba za su iya samar da dimukuradiyya ba. Na gamsu da batun cewa hanyar da za a samu zaman lafiya ita ce samun dimukuradiyya a ko ina, ‘’ in ji shi.

Dangane da dangantakar Amurka da Rasha, shugaba Bush bai yi magana kai tsaye kan banbanacin da ke tsakaninsu ba kan zaben da akai rikici a kansa a Ukraine ba. Amma ya jaddada cewa kyakkyawar dangantakarsa da shugaba Vladimir Putin ya ba su damar magance matsalar cikin sauki da girmamawa. Ya kuma bayyana dangantakar Amurka da Rasha a matsayin mai wahalar fahimta ya kuma ce kasashen biyu na aiki tare a yaki da ta’addanci. Ya kuma jaddada cewa dangantakar tana da kyau.

A kan sauran abubuwa kuwa, Mista Bush ya goyi bayan kokarin amfani da hanyar diplomasiya wajen tunkarar maganar makaman kare-dangi na Koriya ta Arewa da kuma Iran. Ya kuma ce ya gamsu sakataren tsaro Donald Rumsfeld yana yin aiki mai kyau duk da irin kushewar da ya ke samu daga wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka. Mista Bush ya ce manufarsa ga majalisa a shekara mai zuwa zai kasance harkokin cikin gida ne za su zama a kan gaba, wanda ya ce za su hada da farfado da shirin gwamnati na amfani da wani asusun haraji na musamman dan ba wa tsofaffi fansho. Shugaban ya kuma ce kasafin kudin gwamnatin tarayya da zai kai wa majalisar kasa a watan Fabarairu zai magance gibin da ake fama da shi. Ya kuma ce kasafin zai kunshi tsarin kashe kudi wanda zai yi la’akari da bukatun lokutta ya kuma bayar da kudin da zai isa a kare Amurkawa.

XS
SM
MD
LG