Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An halaka Amurkawa goma sha tara a Mosul - 2004-12-22


Fashewar nakiyoyi a cikin wani tantin sojan Amurka a wani sansaninsu na kusa da birnin Mosul a kudancin Iraqi ya halaka akalla mutane ashirin da biyu ya kuma raunata sama da mutane sittin. Akalla Amurkawa goma sha tara na cikin wadanda suka halakan. Harin, ya zo a dai-dai lokacin da firaministan Birtaniya ya kai ziyarar ba za ta zuwa Bagadaza. Daruruwan dakarun Amurka sun zauna kenan suna shirin cin abincin rana sai kawai wata fashewa mai karfi ta girgiza dakin cin abincin. Wani dan jarida wanda ya ke wurin lokacin da abin ya faru ya ce sojojin sun farafadi bayan da wuta ta kama tantin da suke ciki.

Kwamandan dakarun Amurka a garin Mosul, Birgediya-Janar Carter Ham ya ce fashewar wani abu guda mai karfin gaske ne ya abku a dakin cin abincin. Ya ce ana binciken dalilin abkuwar wannan abu. Janar din ya kuma ce wadanda suka mutun sun hada da sojojin Amurka da ‘yan kwangila ‘yan kasashen waje da kuma sojojin Iraqi.

‘’Hakika wannan abin bakin ciki ne to amma kamar yadda sojojin Amurka suka saba sun mayar da martani ga harin kamar yadda ya kamata cike da jarunta da kuma damuwa kan halin da wasu ke ciki, ‘’ in ji shi. A wata sanarwa ta hanyar intanet, rundunar sojan Ansar al-Sunna mai alaka da al-Qaida ta dauki nauyin kai harin, ta kuma kira shi ‘harin shahada’’. Ita wannan kungiya ita ce ta dauki nauyin sare kan wasu ‘yan kasar Nepal goma sha biyu wanda ta yi garkuwa da su a watan Agusta. A lokacin da ya ke magana da ‘yan jarida, bayan taro da sojojin Amurka da suka samu raunuka a asibitin soja na Walter Reed, shugaba Bush ya aike da sakon ta’aziyarsa ga iyalan wadanda suka mutun.’’ Wannan lokaci, lokaci ne na juyayi ga iyalai a lokacin da muka doshi bukukuwan kirsimeti. Muna yi musu addu’a . Muna kuma yi wa masoyansu wadanda ke cikin wani hali a yanzu ta’aziya. Muna so su sani cewa wannan aiki na samar da zaman lafiya ne. Kokarin samar da dimukuradiyya a wurin da a da ke cike da zalunci da kiyayya da barna wani lokaci ne mai cike da fata a tarihin duniya, ‘’Mista Bush ya ce. Harin wanda ya zo a lokacin da firaministan Birtaniya, Tonyn Blair ya kai ziyara Bagadaza a inda suka tattauna da firaministan Iraqi na rikon kwarya, Iyad Allawi kan zaben kasar na watan gobe.

A ranar lahadi ne dai aka kashe ma’aikatan hukumar zaben kasar Iraqi guda uku a Bagadaza, wadanda Mista Blair ya bayyana a matsayin jarumai. Mista Blair ya ce wannan hare-hare na kafin zabe aikin ‘yan ta’adda ne a kokarinsu na hana samar da dimukuradiyya a Iraqi. A wani labarin kuma, ‘yan tawayen Iraqi sun sako’yan jaridun Faransa biyu, Christian Chesnot da Georges Malbrunot wadanda ake garkuwa da su tun a watan Agusta. Wata kungiya mai kiran kanta rundunar sojan musulunci ta Iraqi ta yi barazanar kashe su muddin gwamnatin Faransa ba ta soke dokar hana sa hijabi a makarantun gwamnati ba.

XS
SM
MD
LG