Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Palasdinawa na zaben kananan hukumomin yankin birni - 2004-12-23


A yau Alhamis ne Palasdinawa ke jefa kuri’a a zaben kananan hukumomin cikin birni wanda shine irinsa na farko tun sama da shekaru ashirin da takwas da suka wuce. Akwai alamun fitowar masu kada kuri’a da dama a yankuna ashirin da shida na yamma da kogin Jordan inda ake da ‘yan takara kusan dubu daya masu takarar kujeru dari uku na majalisun yankin. Zaben kananan hukumomin na karshe an yi shi ne a cikin shekarar alif da dari tara da saba’in da shida.

Wannan zabe na Alhamis wani share fage ne ga zaben shugaban kasa da za a yi a ran tara ga watan Janairu na sabuwar shekara wanda za a zabi wanda zai maye marigayi Yasser Arafat, a matsayin shugaban hukumar mulkin Palasdinawa.

Wannan zabe ana ganinsa a wani mataki mai mahimmanci wajen kafa kasar Palasdin. Firaminista Ahmed Qureia ya yi maganganu da dama bayan da ya kada kuri’arsa a garin Abu Dis na yamma da kogin Jordan wanda ke wajen birnin Jerusalem. Ya kuma ce wannan zabe wata alama ce ta fara zaben dimukuradiyya a kasarsu. An samu matsaloli da dama wadanda suka hada da rashin bude tasoshin zabe a kan lokaci saboda rashin kawo kayan zabe da wuri. Amma kuma akwai alamun kokarin bangarorin ‘yan siyasa na ganin sun tura magoya bayansu sun fita kada kuri’a.

A garin Jericho na yamma da kogin Jordan, ‘yan siyasa sun rika amfani da motocinsu wajen kai mutane tasoshin zabe don su samu kuri’unsu. Wannan zabe shine na farko tun zaben shugaban kasa na alif da dari tara da casa’in da shida a inda aka zabi marigayi Yasser Arafat a matsayin shugaban hukumar mulkin Palasdinawa. Ana ganin wannan zabe a matsayin ma’aunin irin goyon bayan da babban bangaren Fatah ta PLO da kuma dan takararta, Mahmud Abbas ke da shi. Wani binciken sanin ra’ayin jama’a na kwanannan ya nuna cewa Fatah ce ke da rinjayen goyon bayan Palasdinawa a inda ta samu kashi arba’in da biyu maimakon ashirin da shida na watan Yuni.

Bangaren siyasar masu zafin ra’ayi na Hamas ya yi kasa a farin jini daga ashirin da biyu zuwa ashirin a wannan binciken. Ana sa ran a shekara mai zuwa mutane miliyan daya da dubu dari biyu za su yi zabe a sauran garuruwa da kauyuka dari shida na Palasdin.

XS
SM
MD
LG