Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rumsfeld ya kai ziyarar ba za ta Mosul - 2004-12-24


Sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld ya kai ziyarar ba za ta zuwa sansanin sojan Amurka da ke kusa da birnin Mosul na Iraqi, wurin da 'yan tawaye suka kai kazamin hari ranar talata. Sakatare Rumsfeld a ranar Juma'a ya gayawa sojojin runduna ta ashirin da biyar ta sojan kasa cewa za su samu nasara kan 'yan tawayen Iraqi. Tun da farko ya shaidawa 'yan jaridar da ke tafiya tare da shi cewa ya kai wannan ziyara ne don ya godewa dakarun Amurka da kuma yi mu su fatan bikin sallar kirsimeti.

Ziyarar ta zo a lokacin da hukumomi ke bincikar yadda dan kunar bakin wake ya samu ya shiga har cikin sansanin ya kuma kashe mutane ashirin da biyu. Kwamandan sojin Amurka a Mosul, Birgediya-Janar Carter Ham ya ce masu binciken sun yi imani cewa wanda ake zargin ya kai harin ya sanya irin tufafin sojan Iraqi ne.

A ranar Alhamis ne sojojin Amurka suka kai lugudan wuta kan 'yan tawaye a Fallujah a lokacin da iyalai sama da dari biyu ke kokarin komawa cikin birnin a karon farko tun hari kan 'yan tawayen don murkushe su na watan Nuwamba.

XS
SM
MD
LG