Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kai harin bam ofishin shugaban mabiya Shia - 2004-12-27


Hukumomin Iraqi sun ce akalla an kashe mutane goma sha uku a wani harin kunar bakin wake da aka kai cikin wata mota kan wani shugaban wata jam'iyyar siyasa ta musulmi mabiya Shia. Shugabannin jam'yyarsa sun ce, shugaban babbar majalisar kungiyar Islamic Revolution a Iraqi, Abdul Aziz al-hakim ya isira ba tare da rauni ba amma harin na ranar litinin ya kashe masu gadinsa da dama.

A wata sabuwa kuma, wata jama'iyyar mabiya Sunni mai girma ta bayar da sanarwar janyewarta daga babban zaben kasa na talatin ga watan Janairu. Mohsen Abdel ya ce jam'iyyar Iraqi Islamic Party ta janye daga zaben saboda hukumomi sun kasa samar da yanayin da za ta iya shiga zaben. Da dama daga cikin shugabannin musulmi mabiya Sunni na kiran da a daga zaben suna cewa yanayin rashin tsaro a kasar zai hana masu zabe fitowa don kada kuri'unsu.

XS
SM
MD
LG