Shugaban kasar Indonesia ya ce kasashen yankin tekun India na kokarin samar da na’urar gano alamun igiyar ruwa mai karfin gaske ta tsunami a yankin. Wannan sanarwa ta zo a lokacin da adadin wadanda suka mutu ‘yan Indonesia ya kai dubu dari shi kuma na jumullar wadanda suka mutu ya kai dubu dari da hamsin. Shugaba Susilo Bambang Yudhoyono a ranar litinin ya ce Indonesia za ta hada karfi da sauran kasashen yankin tekun India don samar da wannan na’ura ta gano tsunami. Gwamnatin Thailand ta ce wannan na’ura na da mahimmancin gaske.
‘’ Za mu kuma yi tunanin samar da na’urar sa ido da gano tsunami a yankin tekun India wanda yanzu babu ita,’’ in ji Sihasak Phuangketkeow, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Thailand.
Thailand ita ce kasar da sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell zai fara isa a yau litinin. Powell zai yi kwanaki yana ziyarar kasashen da suka hadu da bala’in girgizar kasa da kuma igiyar ruwa mai karfi ta tsunami a ranar ashirin ga watan Disamba. A ranar Alhamis zai halarci wani taro kan bayar da agaji wanda za a yi a Jakarta.