Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abbas ya lashe zaben kasar Palasdinu - 2005-01-10


Sakamakon zabe ya nuna a fili cewa dan takara Mahmoud Abbas ne ya lashe zaben shugaban kasar Palasdinu. An kara awa biyu a kan lokacin rufe tashoshin zabe don bayar da dama ga masu zabe su kada kuri’unsu. Sakamakon ya nuna cewa dan takarar Fatah, Mahmoud Abbas ya lashe zaben da kashi sittin da shida zuwa saba’in na adadin kuri’un da aka kada. Mai bi masa , Mustafa Bourghouti ya samu kashi ashirin.

Binciken jin ra’ayin masu zabe dama a kowane lokaci ya nuna Mista Abbas a kan gaba. Idan aka tabbatar da wannan sakamako a ranar litinin to tsohon firaministan zai samu damar aiwatar da shirin sauye-sauyensa na siyasa da kuma shirin diplomasiyyan samar da zaman lafiya tsakanin Palasdin da Isra’ila.Amma ministan gwamnatin Palasdinu, Nabil Shaath ya yi tsokacin cewa ba lallai ne a samu wani sauyi cikin sauri ba.

Ya ce, ‘’bana son mutane su zama cike da fata da yawa. Ba na jin gobe-gobe za mu samu kasarmu. Zai dauki lokaci kuma zai bukaci kokarinmu da na kasashen duniya don su sanya Isra’ila ta amince da shirin taswirar samar da zaman lafiya ta kuma amince ta janye daga kasarmu.’’

Ministan harkokin wajen Israila, Silabn Shalom ya ce Isra’ila na fatan sabon shugaban Palasdinun zai tabbatar da dawowa da shirin samar da zaman lafiya . Ya ce, ‘’daga gobe muna fatan mu fara ganin shirinsu na aiwatar da shirin taswirar zaman lafiya, a mataki na farko. Ba ma son wata kunbiya-kunbiya babu wani kace-nace.’’ Firaministan Palasdinu Ahmed Qureia wanda zai ci gaba da rike mukaminsa a sabuwar gwamnatin ya ce zaben ya nuna irin dagewar Palasdinawa kan kafa mulkin dimukuradiyya. Ya ce, ‘’ mutanenmu na son nunawa duniya cewa ba wai Isra’ila ce kawai mai bin tafarkin dimukuradiyya wannan yankin ba a a muma muna bin tsarin dimukuradiyya.’’

An dai yi zaben lami lafiya kuma an kiyasta cewa kashi sittin da biyar na mutanen da suka isa zabe sun fita zaben. An samu matsalolin rashin kai kayan zabe da wuri a gabashin Jerusalem wanda ya jawo dan rudani.

XS
SM
MD
LG