Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yi gangamin goyon bayan yarjejeniyar samar da zaman lafiya a Sudan - 2005-01-10


Ana sa ran dubannin jama'a za su yi gangamin nuna goyon baya ga yarjejeniyar samar da zaman lafiya don kawo karshen yakin da ya fi dadewa a Afirka. Mataimakin shugaban kasar Sudan, Ali Taha Usman da John Garang na kungiyar SPLM sun sanya hannu kan yarjejeniyar samar da zaman lafiyar a Nairobi. Yarjejeniyar ta biyo bayan tattaunawar shekaru biyu tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyar 'yan tawayen da ke kudancin kasar.

Sun kuma amince da su samar da rundunar soja daya da kuma kafa gwamnatin kawance tare da 'yan kudancin kasar wadanda mafi yawanci kiristoci ne wanda zai tabbatar musu kuma da 'yancinsu nan da shekaru shida masu zuwa. Dukkaninsu sun kuma amince da raba kudaden man fetur da ake samu daga kudancin kasar. Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell wanda ya halarci taron sanya hannun ya nemi bangarorin biyu da su yi amfani da wannan damar don samar da zaman lafiya a yankin Darfur inda ake fama da wani rikicin na daban.Bayan yakin sama da shekaru ashirin da daya fari da cututtuka sun kashe sama da mutane miliyan biyu a Sudan.

XS
SM
MD
LG