Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush ya taya Abbas na Palasdin murna - 2005-01-11


Shugaba Bush ya yi waya don taya Mahmoud Abbas murnar lashe zaben shugabancin kasar Palasdinu ya kuma gayyace shi fadar gwamnati ta White House a Washington. Mai magana da yawun White House, Scott McClellan ya ce a lokacin tattaunawar ta minti goma, shugaba Bush ya yi maganar tattaunawarsu ta baya sannan ya kuma yi bayanin gayyatar da ya yi masa abinda bai yiwa marigayi Arafat ba.

Da aka tambayi Mista McClellan ko shugaba Bush na ganin wata dama ta samun shiga shirin samar da zaman lafiya a Gabas-ta-tsakiya sai ya ce Amurka a shirye ta ke ta traimakawa Palasdinawa wajen aiwatar da sauye-sauyen da suka dace don tabbatar da samun kasarsu mai cin gashin kanta. Ya kuma jaddada cewa a yanzu an bayar da mahimmanaci ne ga taron ministoci wanda aka shirya za a yi a Landan a watan Maris. A wannan taron za a tattauna kan harkar tsaro da inganta tattalin arziki.

Da farko shugaba Bush ya gayawa ‘yan jarida cewa dukkanin bangarorin da abin ya shafa na da gagarumar rawar da za su taka a shirin samar da kasar Palasdinu mai cin gashin kanta tare da ta Isra’ila. Ya kuma ce Isra’ila na sane da mahimmancin zaben ranar lahadi kuma dole ta taimakawa Palasdin don kafa cibiyoyin dimukuradiyya da kuma samar da sauye-sauyenta .

‘’ Isra’ila na da rawar da za ta taka a wurin samar da kasar Palasdin. Kuma yana da kyau shugabannin Palasdin su karfafa matakan tsaronsu don yakar wasu ‘yan kalilan masu kokarin gurgunta Isra’ila , ‘’ya kara da cewa.

Shugaba Bush ya kuma lura cewa zaben Palasdin ya zama wani babi na musanman a sabuwar shekara ga wadanda suka yi imani da ‘yanci da kuma mulkin dimukuradiyya. Ya kuma lura cewa nan da wasu ‘yan makwanni masu zabe za su kada kuri’unsu a Iraqi. Ya ce, ‘’ wanene ya yi zaton yin zabe a Iraqi a dai-dai wannan lokacin a tarihi? Amma ga shi za mu gudanar da zabe a kasar.’’

XS
SM
MD
LG