Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashewar bam ya kashe ‘yan sandan Iraqi shida - 2005-01-11


Jami’an sojan Amurka a Iraqi sun ce akalla ‘yan sandan Iraqi shida ne suka halaka sakamakon fashewar bam a wata mota a garin arewa na Tikrit a ranar talata. Jami’an sun ce ‘yan sanda da dama sun samu raunuka sakamakon wannan hari wanda ake zaton na wani dan kunar bakin wake ne. A wani abu daban kuma, akalla mutane bakwai aka kashe a wani Karamin gari a kudancin Bagadaza. Wadanda suka halakan yawanci fasinjojin wata karamar motar bas ne wadanda ke wucewa a wani yankin da ake kira ‘ triangle of death’’ ( yankin mutuwa).

Kashe-kashen na faruwa ne a lokacin da ‘yan tawaye ke zafafa kai hare-harensu a lokacin da zaben kasar na talatin ga wannan wata ya gabato.

XS
SM
MD
LG