Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai fargabar barkewar kazamin rikici a Darfur - 2005-01-12


Babban jakadan majalisar dinkin duniya a Sudan ya yi gargadin rincabewar rikicin yankin Darfur duk da irin yarjejeniyar samar da zaman lafiya tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen kudancin Sudan. Jakadan na musamman Jan Pronk ya shaidawa kwamitin sulhun majalisar a ranar talata cewa yanayin tsaro a Darfur ba shi da kyau zai kuma iya kazanta muddin ba a dauki mataki ba.

Bayan da ya taso daga Nairobi inda ya halarci taron sanya hannun yarjejeniyar samar da zaman lafiya tsakanin gwamnatin Sudan da ‘yan tawayen kudancin kasar, Mista Pronk ya yi gargadin cewa yanayin da ake ciki a yanzu a Darfur zai iya komawa kazamin yaki. ‘’ Kungiyoyin da su ke dauke da makamai na kara tara makamai. Ana shigar da makamai cikin yankin sabanin matakin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya.

Sababbin kungiyoyin ‘yan tawaye na karuwa kuma suna kai hare-hare a yanki mai wuraren aikin mai na yammacin Kordofan. Za mu iya fadawa cikin halin kazamin yaki muddin ba a dauki mataki cikin gaggawa ba kuma ba a sauya hanyar tunkarar batun ba.’’ Ya ce. Mista Pronk ya bayar da shawarwarin yadda za a magance matsalar. A ciki har da janye batun taimakon agaji da maganar tsaro daga cikin tattaunawar samar da zaman lafiya. Ya kuma bayar da shawarar cewa dukkannin bangarorin biyu da su komar da dakarunsu wurin da su ke a farkon watan Disamba a matakin samar da zaman lafiya.

Shi kuwa jakadan Sudan a majalisar dinkin duniya, Elfatih Mohammed Erwa ya bayyana shawarar raba batutuwan agaji da tsaro daga tattaunawar da cewa abu ne mai kyau amma ya nemi da kasashen duniya da su kara sa matsi a kan ‘yan tawayen.

Jakadan Amurka a majalisar dinkin duniya John Danforth ya yi bayanin cewa ana bukatar matakan gaggawa don hana irin kashe-kashen da aka yi a Darfur a bara. Ya kuma bayar da shawarar cewa tsohon shugaban ‘yan tawayen kudancin Sudan John Garang wanda zai zama mataimakin shugaban kasa a wani shirin samar da zaman lafiya na arewaci da kudancin kasar wani rawar shiga tsakani. Jakadan Amurkan ya kuma nemi kwamitin sulhun da ya yi amfani da barazanar sa takunkumi don a samu nasarar tattaunawar zaman lafiya. ‘’Batun takunkumin har yanzu na kan tebirin tattatunawa, kuma yana da mahimmanci ga dukkanin bangarorin a Darfur su fahimci cewa akwai inda hakuri zai kure kuma maganar sa takunkumi na daya daga cikin abinda za a iya la’akari da shi. Abu na biyu shine batun bayar da wani rawa a siyasance ga John Garang a harkar samar da zaman lafiya a Sudan.’’ Ya kara da cewa.

Jakada Danforth wanda a baya ya yi aikin jakadan shugaba Bush a Sudan ya kuma nemi da a kara yawan dakarun samar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka ta AU a Darfur don hana barkewar rikici. Ya kuma nemi da a kara fadada aikin farar hula masu sa ido na kasar Amurka a Darfur. Kungiyar ta mutane ashirin a yanzu na aiki a wasu wurare a Sudan. Ya kuma jaddada bacin halin da ake ciki a Darfur yana mai goyon bayan samar da zaman lafiya ta kowane hali.

XS
SM
MD
LG