Wani cikakken bincike a wannan makon ya nuna cewa mutane masu yawan cin nama kamar na saniya na iya saurin kamuwa da cutar sankarar hanji fiye da wadanda ke cin abinci mai hade-haden kayan gina jiki. Wannan dogon bincike da aka buga a mujallar kungiyar likitocin Amurka ya yi nazarin yadda mutane ke cin abinci na mutane dubu dari da hamsin daga alif da dari tara da tamanin da biyu zuwa da casa’in da biyu.
An tattara bayanai daga lokacin har zuwa lokacin da aka kammala binciken bayan shekaru goma kuma masu binciken sun gano cewa kashi talatin zuwa arba’in na masu cin naman na cikin hatsarin kamuwa da cutar sankarar hanji da ta dubura fiye da masu cin kifi da naman kaji. Daya daga cikin masu rubuta binciken, Margie McCullough ta kungiyar masu nazarin cutar sankara ta Amurka ta lura cewa binciken ya tabbatar da sakamakon wasu kananan binciken da aka yi a baya. Ta ce, ‘’ Abin da ya bambamta wannan binciken da sauran shine mun yi nazarin dukkanin abincin na lokuta biyu cikin shekaru goma . Saboda haka mun lura da sauye-sauyen da aka samu dangane da abincin da kuma sankarar hanji da ta dubura.’’
A cikin dai wannan mujallar masu binciken sun gano cewa abinci mai cike da ‘yayan itatuwa da ganyayyaki baya hana kare mata daga hatsarin kamuwa da cutar sankarar mama. Wannan binciken ya nuna sabani da sauran binciken baya na kimiyya wanda ya nuna cewa kayan itace da ganyayyaki na hana kamuwa da sankarar mama. Duk da wannan binciken, Madam McCullough ta ce ya kamata mata su ci gaba da cin ‘yayan itatuwa da ganyayyaki.
Ta ce, ‘’kodayake wannan kungiya ba ta yi magana mai karfi ba a kan sankarar mama akwai dalilai da yawa da ya kamata a rinka cin ‘yayan itatuwa da kuma ganyayyaki da yawa domin rage hatsarin kamuwa da cututtuka masu nasaba da ciwon zuciya da kuma sauran nau’in sankara. Kuma akwai dalilai masu dama na cin ‘yayan itatuwa da ganyayyaki Amma ba wai domin hana kamuwa da sankarar mama ba. Ta kuma ce akwai shaida r cewa kiba na da nasaba da sankarar mama a inda cin ‘yayan itatuwa da gayyaki na sa mata su rage kiba.