Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta kudu na son ci gaba da tattauna batun makaman nukiliyar koriya ta arewa - 2005-01-13


Shugaban kasar Koriya ta kudu, Roh Moo-Hyun ya bayyana fatan ci gaba da tattauna batun makaman nukiliyar Koriya ta arewa tsakanin kasashe shida wanda zai kawo karshen matsalar batun makaman. A sakon sabuwar shekara da kuma taro da ‘yan jaridu a fadar gwamnati a Seoul Mista Roh ya ce yanzu akwai yanayin da ya dace na ci gaba da tattuna batun bayan dakatar da shi da aka yi. Ya kuma ce ba zai iya fadar takamaimiyar ranar ci gaba da tattaunawar ba amma ya ce yana fatan za a ci gaba da tattaunawar da zaran an rantsar da shugaba Bush domin yin wa’adi na biyu a kan mulki.

Koriya ta arewa ta kauracewa tattaunawar a watan Satumba bayan da kasar Sin ta dauki bakwancin taron da bai samu nasara ba har sau uku wanda ya hada da Japan da Rasha da kuma Amurka . Koriya ta arewa ta ce tana son gwamnatin shugaba Bush ta sauya yanayinta wanda ta kira na ‘’rashin ya kamata’’ da babban agaji.

Amurka na bukatar Koriya ta arewa ta nunawa duniya cewa a zahiri ta jingine shirinta na kera makaman nukiliya kamar yadda ta yi alkawura karkashin yarjejeniyoyin kasa-da-da-kasa. Shugaba Roh ya lasufta irin matsalar da za a iya samu ta dangantaka tsakanin kasashen biyu amma yace a shirye ya ke da duk wani taro amma y ace da alama shugaba Kim Jong 11 ba zai yadda da wata rana a kusa ba.

Kasashen biyu sun rabu shekaru sama da hamsin da suka wuce kuma ba su taba sanya hannu kan wata yarjejeniya ba tun karshen yakinsu na shekarar alif da dari tara da hamsin da uku. A wani batu kuma Mista Roh ya ce dakarun Koriya ta kudu za su ci gaba da kasancewa a cikin shirin samar da zaman lafiya a Iraqi ko da bayan zaben kasar na karshen wannan watan. Ya ce dakarun za su ci gaba da aiki har sai an samu zaman lafiya a Iraqi. Amma ya ce ba ya zaton zamansu zai dauki wani lokaci mai tsawo.

XS
SM
MD
LG