Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kai harin kunar bakin wake kan ofishin jam'iyyar mabiya SHia a Bagadaza - 2005-01-18


An kai harin kunar bakin wake cikin wata mota kan ofishin wata babbar jam'iyyar mabiya Shia ranar talata a Bagadaza. Jami'an babbar majalisar juyin-juya-halin Islama ta SCIRI sun ce an kashe akalla mutum daya wasu da dama kuma sun samu raunuka. Jam'iyyar wadda ke karkashin shugabancin Abdel Aziz al-Hakim kungiya ce ta 'yan takara mabiya Shia sama da dari biyu masu son tsayawa a zaben talatin ga watan Janairu na 'yan majalisar wucin gadi.

Fashewar bam a hedikwatar jam'iyyar a cikin watan jiya ya halaka mutane goma sha uku. A jiya litinin wasu 'yan bindiga sun sace wani limamin cocin katolika na Syria a Mosul mai suna Basile Georges Casmoussa. Har ila yau 'yan tawaye sun kai hari kan jami'an tsaron Iraq a jiyan a hare-haren da ya halaka akalla mutane ashirin.

Gwamnatin Iraqi ta bayar da sanarwar wani shiri na rufe kan iyakokinta da kuma hana duk wasu motocin da ba na gwamnati ba bin kan tituna a lokacin zaben kasar na talatin ga wata don inganta harkar tsaro. Wata sanarwa daga hukumar zaben kasar Iraqi a ranar talata dinnan ta ce za a rufe kan iyakokin kasar har na tsawon kwana uku daga ranar talatin ga wata kuma motoci masu izinin gwamanati ne kawai za a kyale su bi kan titunan kasar a tsawon lokacin.

XS
SM
MD
LG