Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai 'yan takara da dama a zaben Iraqi - 2005-01-24


A ranar lahadi ne masu jefa kuri'a a Iraqi za su zabi sababbin wakilan majalisar kasar wadda za ta fitar da shugaba da mataimaka guda biyu. Su kuma za su zabi wanda zai kasance firaministan rikon kwarya na gaba. Manyan ‘yan takarar babban mukamin kasar guda uku daga jiha daya su ke wadda a ke sa ran za ta mamaye zaben. Masu zaben za su zabi mutane daga cikin ‘yan takara na jam’iyyu da dama da kuma na wasu kungiyoyin kawance don cike kujeru dari biyu da saba’in da biyar.

Akwai sunayen kungiyoyin jam’iyyu guda dari da goma sha daya a kan takardun zabe da kuma ‘yan takara dubu takwas. Kasancewar kujerun majalisar za a raba su ne bisa irin yawan fitowar masu jefa kuri’a da alama jam’iyyar mabiya Shia ta United Iraqi Alliance ce za ta fi mamaye zaben ranar lahadin. Mabiya Shia ne kashi sittin na jama’ar kasar Iraqi mai yawan mutane miliyan ashirin da shida.

Ita dai kungiyar United Iraqi Alliance an kafa ta ne sakamakon umarnin babban shugaban mabiya Shia na kasar Ayatollah Ali Sistani. Kuma wannan kawancen na karkashin shugabancin wani babban na hannun daman Ayatollah din Abdul Aziz al-Hakim. Mista Sistani wanda ke da goyon bayan mabiya Shia ya kira wannan zabe a matsayin aikin addini kuma ana sa ran kusan kashi arba’in da biyar na mabiya Shia za su fito zaben. Da yake akwai alamun cewa United Iraqi Alliance ce za ta mamaye zaben masu sharhi a Bagadaza na ganin cewa babu mamaki masu neman mukamin firaministan duk ‘yan bangaren kawancen Sistani ne.

Daya daga cikin manyan masu neman wannan mukami shine ministan kudi na wucin gadi a yanzu Abdel Abdul-Mahadi. Dan shekaru sittin da biyu ya yi karatu a Faransa kuma babba ne a babbar majalisar kolin juyin –juya hali ta Islama. Mista Abdul dai ana ganinsa mai sausaucin ra’ayi ya kuma shiga jerin manyan ‘yan takarar ne bayan ganawarsa da shugaba Bush da mataimakinsa Cheney a fadar gwamnati ta White House a watan Oktoban bara. A wata hira da Muryar Amurka Mista Abdul ya yi watsi da labaran da ke cewa tuni an yanke cewa shine zai zama firaminista.

Babban mai bi masa a takarar neman firaministan shine mataimakin shugaban kasa na wucin gadi Ibrahim al-Jaafari. Dan shekaru hamsin da bakwai wanda likita ne amma ya koma siyasa shine babban kakakin kungiyar Islamic Dawa wadda ta yi fito-na-fito da Saddam Hussein a shekarun alif da dari tara da saba’in. Mista Jaafari ya shugabanci jam’iyyarsa ne daga kasar waje kasancewar yana gudun hijira a lokacin. Ya kuma kasance dan siyasar da ya fi shahara a bangaren mabiya Shia a Iraqi.

Wani kuma babban dan takarar mukamin firaminista a Iraqin shine Hussein al-Shahristani wanda na daya daga cikin mutane shida da Ayatollah Sistani ya zaba don su fitar da ‘yan takarar United Iraqi Alliance. Shahristani masanin kimiyyar nukiliya ne wanda ya samu horonsa a Kanada ya kuma yi zaman gidan kaso a lokacin mulkin Saddam Hussein bayan da ya ki amincewa ya shiga aikin shirin nukiliyar Iraqi. A yanzu ana ganin shine babban na hannun daman Ayatollah Sistani Sai dai masu sa ido sun ce da alama cewa masanin kimiyyar bai nuna damuwa kan zama firaministan ba amma zai iya karbar mukamin idan an ba shi.

Kodayake ya danganta kan irin yadda sakamakon zaben zai kasance da alama duk ‘yantakarar kungiyar Alliance din za su gamu da kalubale sosai daga firaministan rikon kwarya na yanzu Iyad Allawi. Allawi ya tara mabiya masu sausaucin ra’ayin addini don jan hankalin ‘yan Iraqi wanda ba sa son addini ya yi tasiri a siyasar kasar. Na hannun daman Allawi suna hasashen cewa idan mabiyansa suka samu kashi saba’in ko sama da haka na kujeru dari biyu da saba’in da biyar na majalisar Mista Allawi wanda mabiyin Shia ne zai iya samun goyon bayan da zai ci gaba da zama a kan matsayin firaminista.

XS
SM
MD
LG