Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush ya nemi ‘yan Iraqi da su yi watsi da ‘yan ta’adda - 2005-01-27


Shugaba Bush ya nemi ‘yan Iraqi da su yi watsi da barazanar ‘yan ta’adda su kuma fito su kada kuri’unsu a babban zaben kasar na ranar lahadi. Bush ya ce wannan zabe muhimmin abu ne ga wadanda suka yi imani da ‘yanci. Kwana hudu kafin babban zaben ya gayawa Amurkawa cewa yana goyon bayan shirin zaben. Ya ce mutanen Iraqi da dama na son kada kuri’unsu amma suna jin tsoro. ‘’Ina son kowa da kowa ya kada kuri’a. Ina son a yi watsi da ‘yan ta’adda. Wadannan ‘yan ta’adda ba su da kishin mutanen Iraqi. Ba su da wata manufa mai kyau. Ba su da alkibla kan kyakkyawar makoma.’’ In ji shugaba Bush.

Mista Bush ya kuma ce ‘yan tawayen dai sun kaddamar da yaki ne kan ‘yan kasarsu. Ya kuma sha alwashin cewa za a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara ya kuma yi hasashen samun nasarar zaben. Ya ce, ‘’ miliyoyin ‘yan Iraqi za su nuna jarumtakarsu da son kasarsu da kuma sha’awarsu ta samun ‘yanci.’’ Shugaban ya yi tsokaci da jawabinsa na kama aiki a wa’adi na biyu na ranar Alhamis kan maganar ‘yanci da kuma yaki da zalunci. A lokacin da ya ke hira da ‘yan jaridu a karon farko bayan da ya kama mulki a wa’adi na biyu Mista Bush ya jaddada cewa a lura da irin nasarar da za a samu nan gaba na yada ‘yanci ba wai irin matsalar da ake fama da ita ba a yanzu. Mista Bush ya ce idan ba a samu hakan ba to Gabas-ta-tsakiya za ta ci gaba da zama dandalin kyama da kiyayya da kuma wani fagen horar da mutane masu manufa ta daban da ta su.

Da aka tambayi Bush kan ta yadda zai yada manufarsa ta ‘yanci zuwa sauran kasashen da Amurka ke da alakar tattalin arziki ko tsaro mai karfi sai ya ce za a iya ci gaba da irin wannan alaka a kuma lokacin da ake tattauna batun mutunta hakkin dan Adam. Ya kuma yi magana kan tattaunawarsu da shugabannin Sin da Rasha. ‘’ A tattaunawarmu da shugabannin duniya don maganta matsalolin yau zan gaya musu cewa babbar hanyar samun ci gaba ita ce ta dimukuradiyya.’’ Ya ce. Mista Bush ya yi watsi da kushe manufofinsa kan kasashen waje daga bangaren ‘yan Demokrat a inda ya kuma lura cewa kalamansu ka iya kawo shakku a zukatan ‘yan Iraqi kan manufar Amurka a kasarsu. Ya ce ya kamata masu goyon baya da kuma wadanda ba su goyon baya su kalli lamarin da idon basira. ‘’A yanzu dubi irin abin da ya faru a cikin dan gajeren lokaci: zaben Afghanistan da na Palasdin wadanda zabuka ne masu kyakkyawan fata, haka kuma na Ukraine ga kuma na Iraqi. Hakika muna ganin tarihi mai ban sha’awa,’’ in ji shugaba Bush.

Shugaba Bush ya kuma ce yana da abubuwa da yawa da zai fada a ranar laraba mai zuwa a lokacin da zai yi jawabin kasa na shekara-shekara.

XS
SM
MD
LG