Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karzai ya nemi ‘yan Iraqi da su fito zabe - 2005-01-28


A lokacin da ‘yan Iraqi ke shirin gudanar da babban zaben kasa, shugaban Afghanistan Hamid Karzai ya yi kira a garesu da su fito kwansu da kwarkwatarsu su kada kuri’unsu domin zama shugabannin kansu. A lokacin da ya ke magana da ‘yan jaridu a ranar Juma’a Mista Karzai ya nemi ‘yan Iraqin da su yi koyi da kasarsa su kuma nuna juriya da duk wani tashin hankali su kada kuri’unsu

Afghanistan dai ta gudanar da zabenta na farko a cikin watan Oktoban bara cikin lumana duk da fargabar hare-hare daga marasa goyon bayan gwamnati. Shugaba Karzai ya ce gudanar da zaben ya kunyata ‘yan tawaye marasa goyon bayan shirin kafa mulkin dimukuradiyya. 'Wannan abu ya zama nasara kan duk wadanda ba sa son Afghanistan ta zauna lafiya ta kuma samu karuwar arziki.’’ Ya ce. Kodayake Iraqi na fuskantar babban kalubale fiye da Afghanistan Mista Karzai ya ce zaben dole ne a kokarin ceto Iraqi daga rikice-rikicen yaki. Ya ce,’’ gudanar da zabenne hanyar da ‘yan uwanmu ‘yan Iraqi za su samu gwamnatin da su ke so su kuma samu zaman lafiya da karuwar arziki.’’

Da Iraqi da Afghanistan na da tarin dakarun kasashen waje a cikin kasashensu. Amma shugaba Karzi ya ce yin zaben ne kawai zai sanya Iraqi su mulki kansu da kansu. Shugaban na Afghanistan ya yi wadannan kalaman ne bayan dawowarsa daga ziyarar aiki zuwa Iran. Ya bayyana cewa ziyarar ta samu nasara a inda ya bayar da misalin shirin sayan wutar lantarki daga Iran don samar da wuta ga yammacin birnin Afghanistan na Herata da kuma shirin inganta jigilar hanyar mota tsakanin kasashen biyu.

XS
SM
MD
LG