Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firaministan Georgia ya rasu sakamokon iska mai guba - 2005-02-03


Firaministan Georgia Zurab Zhvani ya rasu da alama sakamakon shakar iskar gas mai guba. Ya rasu yana da shekaru arba'in da daya. Ministan cikin gida Vano Merabishvili ya ce an samu Mista Zhvania a mace a safiyar Alhamis a wani gida da ke Tbilisi mallakar abokinsa. Ya kuma ce ga dukkanin alamu wani hadarin gubar gas ne ya yi sanadiyar mutuwar kuma an kai gawarsa zuwa ofishin mai bincike. Mista Merabishvili ya ce masu tsaron lafiyarsa sun damu kasancewar ba ya amsa waya saboda haka suka balla taga suka shiga a inda suka tarar da Mista Zhavnia da abokinsa duk a mace.

An haifi Zhavania a shekarar alif da dari tara da sittin da uku a Tbilisi kuma tsohon dan majalisar dokokin kasa ne wanda shugaba Mikhail Saakasvil ya nada a matsayin firaminista a watan Janairun shekara ta dubu biyu da hudu.

XS
SM
MD
LG