Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra’ila ta saki fursunoni ‘yan Palasdinu dari biyar - 2005-02-22


Da sanyin safiyar Litinin ne Isra’ila ta fara sakin fursunoni ‘yan Palasdin daga kurkukun Etzion wadanda tuni suka doshi gidajensu a yankin yammacin kogin Jordan da kuma yankin zirin Gaza. Dukkanin wadanda aka saki an nemi da su sanya hannun alkawarin cewa ba za su sake shiga harkar ta’addanci ba.

Gwamnatin Isra’ila ta amince ta sako fursunonin ne a farkon wannan watan saboda irin kyakkyawar fata da Israi’la ke yi wa sabon shugaban Palasdin Mahmoud Abbas. Ana sa ran za a kara sakin wasu fursunoni ‘yan Palasdin guda dari hudu nan da ‘yan makwanni masu zuwa. Wani kwamitin kasashen biyu ne ake sa ran zai fitar da sunayen wadanda za a sakin. Haka kuma wasu Palasdinawa talatin da tara wadanda aka kore su zuwa yankin zirin Gaza da kuma Turai an amince da su dawo yankin yammacin kogin Jordan. Sakin fursunonin ya zo kwana daya bayan da gwamnati ta amince ta rushe dukkanin matsugunan Yahudawa ‘yan kaka-gida da ke Gaza.

Firaministan Isra’ila Ariel Sharon ya ce matakin yin hakan mai wuyar gaske ne. ‘’A dukkann irin tsawon shekarun da na yi ina aiki na dauki matakai daruruwa koma dubanni wasu ma sun shafi rayuwa da mutuwa amma wannan matakin janyewa shine mai wahalar gaske, ‘’ ya ce.

Firaministan ya kuma ce ya gamsu wannann matakin janyewa shine mafi a’ ala domin tabbatar da wanzuwar Isra’ila mai bin tafarkin dimukuradiyya. Sakamakon jefa kuri’ar amincewar firaministan ya sanya hannu don bayar da izinin tashin matsagunan Yahudawa daga yankin Gaza da kuma wasu yankuna hudu na yamma da kogin Jordan. Dokar ta ba mazauna wuraren watanni biyar da su tashi ta kuma tanadi wani hukunci mai tsauri kan duk wanda ya ki tashi nan da wa’adin ashirin ga watan Yuli.

Shugaban hukumar mulkin Palasdinawa Mahmoud Abbas ya ce hukumarsa za ta tabbatar da janyewar cikin lumana ba tare da tashin hankali ba daga Palasdinawa. Ya kuma ce Palasdinawa za su za su rinka jefa fulawowi ga Yahudawan da suke janyewa maimakon duwatsu. Majalisar ministocin Isra’ila ta kuma amince da a sake nazarin shingen da ake ginawa a yankin yammacin kogin Jordan don barin yankin Palasdinawa ne. Yanzu shingen zai hada da kashi shida ne kawai na yammacin kogin Jordan maimakon kashi goma sha biyar karkashin shirn farko. Amma duk da haka akwai korafi daga bangaren Palasdinwa kan cewa an mamaye musu yankunansun kuma ce ya saba yarjejeniya kan iyakoki.

XS
SM
MD
LG