Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush na shirin tattaunawa da shugabannin Turai - 2005-02-22


Shugaba Bush ya fara wani jerin tattaunawa da shugabannin Turai a Brussels a kokarinsa na kara gyara dangantakar da ta yi tsami sakamakon yakin Iraqi. Shugaba Bush zai kwashe kusan ranar yau ne a wajen taron tattaunawa da farko da shugabannin kungiyar NATO sai kuma na Tarayyar Turai.

Batutuwan da za su tattauna na da dama. In kuma aka yi la’akari da jawabin shugaban ga mutanen Turai na jiya za a ce tattaunawar za ta ba da karfi kan samar da zaman lafiya a Gabas ta tsakiya. Kokarin kawo karshen rikici tsakanin Isra’ila da Palasdinu na da mahimmancin gaske ga firaminista Tony Blair na Birtaniya wanda ke shirin karbar bakuncin wani babban taron samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya ranar daya ga watan Maris a Landan.

Mista Blair wanda babban abokin Amurka ne a shirin kawancen kai hari kan Iraqi ya hadu da shugaba Bush a lokacin karin kumallo kafin su wuce zuwa hedikwatar kungiyar NATO. Ya kuma ce akwai kyakkyawan fata kan shirin samar da zaman lafiya a Gabas ta tsakiya ‘’Da wannan taron tattaunawa na Landan a mako mai zuwa ina ga muna da damar samun mafuta wanda ina ga zai yiwa kasashen duniya amfani, ‘’ in ji Mista Blair. A lokacin da ya bayyana gaban ‘yan jarida na wani dan lokaci firaminista Blair ya yi magana kan mahimmancin kyakkyawar dangantaka tsakanin Turai da Amurka . Mista Bush ya ce akwai mahimmancin samun karkarfar Turai a wannan kokaci.

‘’Ina fatan ganin an yi wannan taro na yau. NATO na da mahimmanci ga dangantakar Amurka da kuma Turai. Ina kuma fatan ganin irin wannan taro da Tarayyar Turai . Kuma kamar yadda na fada a jawabi na na jiya karkarfar Tuarai na da mahimmanci ga Amurka, kuma da gaske nake,’’ in ji Bush. Dukkanin kasashe ashirin da shida na kungiyar NATO na halartar wannan taro a hedikwatar kungiyar. Kuma yawancin shugabannin gwamnatocin da ke halartar taron za su kuma shiga taron Tarayyar Turai.

Ana yin tarurrukan ne a lokacin da ake ta fama da kame-kame a babban birnin Belgium. Akan dai dauki tsauraran matakan tsaro a lokacin tarurruka amma kasanceawar akwai shugabannin kasashe da dama ya sanya gwamnatin Belgium daukar karin matakan tsaro.

XS
SM
MD
LG