Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar mabiya Shia a Iraqi ta zabi Jaafari don takarar firaminista - 2005-02-23


Babbar jam’iyyar kawancen mabiya Shia a Iraqi ta zabi wani tsohon likita mai dangantaka ta kut da kut da Farisa a ranar Talata a matsayin dan takarar mukamin firaminista. Zabar Mista Jaafari don yin wannan takarar ya nuna alamar cewa mabiya Shia ne za su fara fitar da shugaban Iraqi a karkashin zababbiyar gwamnati tun bayan shekaru hamsin.

Kawancen United Iraqi Alliance ta mabiya Shia wadda ta lashe kashi arba’in da takwas na kuri’un da aka kada a zaben kasar na talatin ga watan Janairu ta fitar da Mista Ibrahim al-Jaafari mataimakin firaministan gwamnatin rikon kwarya a matsayin dan takararsu a mukamin firaminista.

Mista Jaafari wanda likita ne dan shekaru hamsin da takwas na da sassaucin ra’ayin addinin Musulunci kuma ana girmama shi ya kuma yi zaman gudun hijira a Landan. Mista Jaafari na kuma da kusanci da yan Sunni ana ganinsa a matsasyin wanda ka iya hada kan sabuwar gwamnatin da za a kafa. Babban mai kalubalantarsa shine firaministan rikon kwarya Mista Iyad Allawi wanda ‘yan bangarensa suma suka tsayar da shi takarar. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Richard Boucher ya ce zabar Mista Jaafari don yin wannan takara wani mahinmin mataki ne a fasalin siyasar Iraqi.’’ Muna fatan mu yi aiki da kowace irin gwamnati aka kafa a Iraqi. Ba wai kawai firaminista ba a’a har ma shugaban kasa da ministoci .Kuma muna fatan kyakkyawar dangantaka da sabuwar gwamnatin rikon kwaryar,’’ ya ce.

An zabi Mista al-Jaafari ne a matsayin dan takarar mukamin firaminista karkashin kawancen jam’iyyun mabiya Shia bayan da wani mai yin takarar Ahmad Chalabi ya janye daga takarar.Mista Chalabi wanda mai sassaucin ra’ayin Shia ne ya samu goyon bayan hedikwatar tsaron Amurka ta Pentagon kafin mamayar Iraqi amma tuni sun yi hannun riga da Amurka saboda zargin mika wasu mahimman bayanai ga Iran. Kungiyar kawancen jam’iyyun mabiya Shia ta lashe kujeru dari da arba’in cikin kujeru dari biyu da saba’in da biyar a majalisar dokoki ta kasa amma tana bukatar kawance da kananan jam’iyyu kafin ta samu damar kafa sabuwar gwamnati.

Ana bukatar kuri’un kashi biyu cikin ukun ’yan majalisar dokokin kafin a dauki mahimman matakai wanda ya hada da zabar firaminista. Dole ne bangaren ‘yan mabiya Shia su tattauna da kungiyar Kurdawa ta Kurdish Alliance mai kujeru saba’in da biyar a majalisar dokokin. Sai dai tattaunawar ka iya daukar makwanni da dama.

XS
SM
MD
LG