Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush ya ce gabashin Turai na yada ‘yanci a duniya - 2005-02-24


Shugaba Bush ya ce mutanen gabashin Turai wadanda a baya suka zauna karkashin mulkin kwaminis a yanzu na yada sakon ‘yanci a duniya. A jawabinsa ga mutanen Slovakia ya yabawa kasar kan rawarta wajen samar da dimukuradiyya mafi sabinta a duniya a Iraqi.

Dubannin ‘yan Slovakia sun taru a babban dandalin Bratislava don sauraran shugaban.Duk da sanyin da ake fama da shi karbar ta yi armashi a lokacin da shugaba Bush ya yi tsokaci kan abinda ya faru shekaru goma sha bakwai da suka wuce lokacin da hukumomin ‘yan kwaminis a tsohuwar kasar Czechoslovakia suka tarwatsa taron jama’a masu zanga-zanga suna dauke da kyandiran ‘yanci, hasken da ya yadu har wajen Bratislava.

Ya ce,’’ da kuka nemi ‘yancinku kun kawo sauyi wanda ya ‘yantar da kasarku ya kuma kawo sauyi a nahiyar.’’ Shugaban ya lura cewa Slovakia wadda yanzu mamba ce a kungiyar NATO ta aika da dakarun samar da zaman lafiya a Kosovo da kuma msau sa ido kan zabe a Ukraine da kuma dakaru dari zuwa Iraqi. ‘’Kun nuna cewa karamar kasa wadda ta kafu a kan babbar manufa na iya yada manufar ‘yanci a ko ina a duniya,’’ ya ce.

Mista Bush ya kuma ce an kawo, karshen mulkin ‘yan kwaminis a Czechoslovakia ne a alif da dari tara da tamanin da tara a inda kasar kuma ta rabu biyu a hankali bayan wasu ‘yan shekaru. Ya kuma ce ‘yan Slovakia da duk ‘yan gabashin Turai sun fahimci amfanun samar da ‘yanci a Iraqi sun kuma ji dadin ganin hotunan ‘yan Iraqi na rawa a kan titina bayan kada kuri’unsu a watan jiya. ‘’Ga mutanen Iraqi wannan ita ce shekarar alif da dari tara da tamanain da tara dinsu kuma a kullum za su tuna da wadanda suka tsaya musu a kokarin neman ‘yanci, ‘’ in ji shugaba Bush. Wannan jawabi wani share fagen tattaunawar shugabanne da shugaba Vladamir Putin na Rasha.

Wannan ziyara ita ce ta farko da wanim shugaban Amurka ya kai zuwa Bratislava kuma ita ce ta karshe a ziyar shugaban zuwa kasashen Turai. An dauki tsauraran matakan tsaro a babban birnin Slovak a lokacin ziyarar musammanma a wurin da za a yi tattaunawar tsakanin shugabannin biyu.

XS
SM
MD
LG