Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Palasdin ta amince da sababbin ministoci - 2005-02-25


Bayan tsawon lokaci ana mahawara da kuma kulle-kullen siyasa majalisar dokokin Palasdin ta amince da nadin ministoci ashirin da hudu karkashin firaminista Qureia. Yar majalisa Hanan Ashrawi ta ce sabuwar gwamnatin ba lalle ne ta zama mara kurakurai ba to amma dai mataki ne da ya dace. ‘’ Mun nunawa mutanen Palasdin cewa sauye-sauyenmu na kan turba kuma akwai bangarorin gwamnatin daban-daban da bin doka da kuma cikakkiyar dimukuradiyya .

Wannan shine abinda muke so’’, in ji Madam Ashrawi Yan majalisar sun ki amincewa da sunayen da firaminista Qureia ya tura da farko a inda suka nemi da a kawo sunayen sababbin fuska a harkar gwamnati wanda za su kawo sauye-sauye a harkar mulki wadanda ba a zarginsu da cin hanci da rashawa. Sau biyu ‘yan majalisar na kin amincewa da sunayen da firaministan ya tura musu kafin wannan amincewa ta ranar Alhamis. Sunayen ministocin ya hada da sababbi goma sha bakwai kuma dukkaninsu kwararru a fannoninsu kyuma masu manyan digirori.

Wannan amincewar ta nuna wata nasara ce ga sabon shugaban Palasdin Mahmoud Abbas da kuma burinsa na kawo sauye-sauye a harkar mulkin Palasdin da kuma shirinsa na samar da zaman lafiya da Isra’ila. Mohammed Shtayeh wanda ya yi aiki a matsayin jami’in kamfen na Mahmoud Abbas yanzu shine ministan gidaje ya kuma gayawa Muryar Amurka cewa wannan amincewa ta nuna wata alama babba ga mutane da kuma gwamnati.

‘’Wannan sako ne da ke nuna sauyi da fata kuma nauyin na kan kowane minister dan tabbatar da an cimma nasara,’’ in ji Mista Shtayeh. Sauran sababbin ministocin sun hada da Nasser al-Kidawa ministan harkokin waje wanda da wakilin Palasdin ne a majalisar dinkin duniya kuma dan dan uwan marigayi Yasser Arafat. An kuma nada tsohon janar Nasser Yousef a matsayin ministan cikin gida kuma shine zai yi aikin sake fasalin hukumomin tsaron Palasdin . Ministan kudi Salam Fayyad ya rike matsayinsa yana rike da wannan mukami ne tun wani tsawon lokaci kuma Amurka na girmama shi haka su ma kungiyoyin ba da taimako.

Tsohon mai sasantawa Saeb Erekat ya rasa mukaminsa na minista amma zai ci gaba da aikin mai sasantawa. ‘’Abu ne mai wahala mun raba dare ba barci amma wannan ita ce dimukuradiyya . An haifar da dmukuradiyyar Palasdin. Kuma wannan ita ce wahalar kuma za mu saba da ita .’’ Ya ce. Ita dai wannan majalisar ministocin Palasdin mataki ne mai mahimmanci ga Palasdin amma za ta yi gajeren wa’adi ne saboda akwai zaben ‘yan majalisar dokoki a watan Yuli wanda zai samar da wata sabuwar gwamnati.

XS
SM
MD
LG