Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilin China kan tattaunawar nukiliya ya isa Seoul - 2005-03-02


Babban jami’in kasar Sin kan tattaunawar rage yaduwar makaman nukiliya ya ki amsa tambayoyin ‘yan jaridu a lokacin da ya isa Seoul a yau Laraba. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Wu Dawei ya isa Seoul ne don tattaunawar kwana uku a kokarin dawo da Koriya ta Arewa kan tebirin tattaunawa. A watan jiya ne Koriya ta Arewa ta janye gaba daya daga tattaunawa kan batun mallakar makaman nukiliyanta. Koriya ta Arewan ta ce ta mallaki makaman nukiliya kuma tana shirin kara samar da wasu.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong 11 daga baya ya gayawa babban jami’in Sin din cewa kasarsa na iya komawa kan tebirin tattaunawa muddin aka cika wasu sharudda. Sai da tsakanin Pyongyang da Beijing babu wadda ta yi cikakken bayani kan wadannan sharuddan. Ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu Ban Ki-Moon ya ce a ranar Laraba yana fatan jin sababbin bayanai da Mista Wu zai yi. Mista Ban ya ce Koriya ta Kudu na da buri da kuma fatan ganin China ta kara kaimi wajen dawo da Pyongyang kan tebirin tattaunawa.

China dai ta gudanar da tattaunawa har sau uku tare da Japan da Rasha da Amurka da Koriya ta Arewa da ta Kudu. A matsayinta na babbar abokiyar Koriya ta Arewa ana ganin China na da tasiri kan shugabannin Koriya ta Arewan.

Amurka na sa matsi kan Koriya ta Arewa kan ta lalata shirinta na nukiliya ta kuma cika alkawarinta na farko ga kasashen duniya kan kawar da nukiliya a duniya. Ita dai Koriya ta Arewa ta ce tana bukatar taimakon tattalin arziki da kuma tabbacin tsaro daga Amurka kafin ta lalata makamanta na nukiliya.

XS
SM
MD
LG